An bukaci Al umma Musulmai da Maida hankali wajen yin Adu o I domin Samar da zaman lafiya a fadin Najeriya.

 









Daga Alhassan Haladu Yola.


A Wani mataki na inganta tsaro da Samar da zaman lafiya da magance matsalar tattalin arziki an kirayi Al umma musulmai da suyi amfani da azumin tasu a da ashura wato Tara da goma ga wata Al Muharam domin Neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalu balen tsaro a fadin kasan Nan baki Daya.



Shugabar kungiyar Yan agaji a  bangaren mata na Jama atul Nasril Islam dake jahar Adamawa, Hajiya Amina Muhammed ce tayi wannan Kira a zantawarta da manema labarai a Yola.



Amina Muhammed tace azutar ranan Tara da goma ga watan Al Muharam suna da matukan muhimmanci ga Al umma musulmai saboda haka Yana da muhimmanci Al umma musulmai su azumci kwanaki biyu tare da yin Adu o I Samar da zaman lafiya dama kawo karshen matsalar tattalin arziki a fadin kasan Nan baki Daya. 


Hajiya Amina ta Kuma shawarci Al umma musulmai da sukasance masu gudanar da aiyukan Alheri da adu o I a cikin lwanakin biyu domin Neman falalan da Lada masu yawa daga Allah madaukakin sarki.



Ta Kuma shawarci iyaye da suyi amfani da wannan lokaci wajen yiwa yaransu Adu o I domin Neman shiriyarsu da Kuma inganta rayuwarsu yadda ya Kamata.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie