Gwamnatin tarayya ta Horan da Yaran Matan Chibok sana o I daban daban a jahar Asamawa.

 




Daga Alhassan Haladu Yola.


Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ma aikatar harkokin mata a Najeriya ta koyawa yaran matan chibok Wanda aka cetosu daga hanun masu garkuwa da mutane sana o I daban daban domin dagaro da kansu.


Yaran mata akalla 18 ne dai suka Samu horon wadanda suka koyi sana o I da suka hada da dinki, da dai sauransu Wanda hakan zai taimaka wajen inganta rayuwarsu yadda ya Kamata.


Bikin yaye yaran matan dai ya gudana ne a Jami ar Modibbo Adama dake Yola a jahar Asamawa.


Da take jawabi ministar harkokin mata a Najeriya Hajiya Imaam Ibrahim Suleiman tace gwamnatin tarayya ta dauki matakin haka ne duba da yadda yaran mata suka tsinci kansu a ciki Wanda haka ya sasu cikin damuwa, saboda haka ya Kamata a koya musu sana o I da zasu dogara da kansu domin inganta rayuwarsu.


Ministan ta Taya wadanda aka yaye murna tare da Kiran su da sukasance masu amfani da abinda aka koya musu ya hanyar da ta dace  domin bunkasa harkokinsu domin su zama abin koyi ga na gaba.


Imaam Ibrahim ta tabbatar da cewa ma aikatar mata a shirye take wajen taimakawa yaran mata a bangarori daban daban domin ganin yaran matan sun Samu inganceccen rayuwa, dama bunkasa tattalin arziki yadda ya Kamata.



Ministan ta Kuma yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tininu bisa kokarinsa na amincewa wajen taimakawa yaran matan na chibok Wanda a cewarsa hakan ya taimaka wajen inganta rayuwar yaran matan.


Ta Kara da godewa Mataimakin shugaban kasa  Kashim Shettima.bisa goyon bayansa kasancewa shine shugaban kwamitin kan harkokin yaran matan na chibok a fadar shugaban kasa, Wanda Shima ya taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa yaran matam.


Ministan ta godewa hwamnatocin jihohi Asamawa da Borno bisa goyon baya da suka baiwa ma aikatar domin ganin an Samu nasaran koyawa yaran matan sana o I daban daban.



A jawabinsa kwamishiniyar harkokin mata a jahar Adamawa Mrs Neido Geoffrey ta yaba da irin wannan na mikin kokari da ma aikatar harkokin mata ta tarayya tayi wajen taimakawa yaran matan.




Neido Geaffrey ta shawarci wadanda suka Samu horon da sun manta da abinda ya faru su daukeshi a matsayin jarabawar ne daga Allah, inda tace wannan taimakon zai taimaka musu wajen inganta rayuwarsu na yau da kullum.



Kwamishiniyar ta tabbatar da cewa ma aikatar harkokin mata a jahar Adamawa na iya kokarinsa domin ganin an samarwa yaran mata sana o in dogaro da Kai domin Samar da cigaban Al umma baki Daya.



Shima anashi jawabi shugaban kungiyar iyaye yaran matan Yakubu Nkeki ya baiyana faraun cikinsa dangane da wannan taimakon da aka baiwa yaransu Wanda acewarsa wannan abun a yabane.




Yakubu yace suyi iyaye suna masu godewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin shugaban kasa Kashim shertima harma da gwamnaticin jihohin Adamawa da Borno dangane da wannan taimakao da sukayiwa yaransu.



Da take jawabi a madadin yaran mata da akayiwa horon Hauwa ta baiyana farin cikinta dangane da wannan tallafi da aka Yi musu Wanda hakan zai taimaka ma rayuwarsu yadda ya Kamata tare da tabbatar da cewa zasuyi amfani dashi yadda ya Kamata domin Samun cigaba.



Bayan kayakin aiki da aka rarraba musu kowannensu ta Samu nera milyon Daya, a yayinda iyayensu Suma kowannensu ya Samu nera dubu Dari biyu, masu Yara daga cikinsu an dauke musu nauyin haran da dai sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie