KUNGIYAR MANOMA ALBASA SUN BUKACI TAIMAKON GWAMNATI DONIN BUBKASA HARKOKIN NMAN ALBASA A JAHAR ADAMAWA.




Daga Alhassan Haladu Yola.


Kungiyar manoma albasa a jahar Adamawa sun kirayi gwamnati da ta Kai musu daukin gaggawa domin su Samu damar bunkasa harkokinsu yadda ya Kamata.


Sakataren kungiyar na kasa Ibrahim Goni Dasin ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a Yola.


Ibrhin Goni Dasin yace kawo yanzu manoma albasa na cikin Wani yanayi na tsadar kayakin noma. Wanda hakan ya haifar musu da koma baya a bangaren noman albasa, Wanda Kuma in ba a dauki matakin gaggawaba to zai iya haifar da karancin albasa a fadin jahar ta Adamawa.



Goni Dasin ya Kara da cewa  tsadar taki, maganin feshi, da dai sauransu yayi sanadiyar koma baya sosai a harkan noman albasa a jahar Adamawa.


Goni yace duk da cewa gwamnatin ta kaddamar da rarraba taki cikin farashin mai sauki Amman haryanzu ba Wani manomin albasa da ya Samu taki. Don haka suna bukatar gwamnati ta Kai musu dauki ta taimaka musu da kayakin noman cikin sauki domin su Samu damar gudanar da harkokinsu cikin sauki ba tare da wata matsalaba.


Ya Kuma kirayi Yan kungiyar da sukasance masu hada kansu a Koda yaushe domin ganin sun bunkasa harkokin noman albasa a fadin jahar Asamawa.


Kawo yanzu dai ana Samun karanci albasa a dukkanin kasuwanni dake fadin jahar Asamawa, Wani lokaci ma sai an shika kamaru ko wasu jihohi domin kawo albasa, lamarin da ya haifar da tsadar albasa a jahar ta Asamawa.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie