An bukaci iyaye su Maida hankali kan karatun yaransu domin ganin sun Samu inganceccen ilimi.
Daga Alhassan Haladu Yola. Wani mataki na inganta ilimi an kirayi iyaye a karamar Hukumar Yola ta rewa da sukasance masu Sanya Ido tare da tura yaransu makarnta Wanda hakan zai taimaka wajen bunkasa ilimi a tsakanin dalube yadda ya Kamata. Shugaban kwalejin Gen. Murtala Muhammed dake Yola Mallam Muhammed Alhaji Musa ne yayi wannan kira a lokacin da ya jagorancin rarrabawa dukkanin makarantu sakandare dake karamar Hukumar Yola ta arewa takardun karatu. Mallam Muhammed Alhaji Musa yace tundra gwamnatin jahar karkashin jagorancin gwamna Ahmadu Fintiri ta taimaka da takarandun karatu wa manyan makarantu sakandare, saboda haka ya Kamata iyaye Suma su Bada tasu gudumawa domin ganin yaran sun Samu inganceccen ilimi yadda ya Kamata. A cewarsa iyaye su suke da Kaso Mafi tsoka wajen tura tare da Sanya Yara makaranta don haka ya Kamata iyaye suyi tunani sosai suka Kara Maida hankali wajen karatun yaransu domin ganin an Samu damar bunkasa ilimi a tsakanin yaran yadda ya Kamata. ...