An yabawa gwamna Fintiri bisa aiyukan cigaban jahar da yayi a cikin kwanaki dari.
A yayinda gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya cika kwanaki dari akan Mulki bayan sake zabensa a wa adi na biyu. Hakan yasa jama a ke baiyana irin kamun ludayin gwamnan a cikin kwanaki dari.
Sunday Wugari mataimakin na musamman na gwamnan kan harkokin jama a Yana daga cikin masu baiyana irin cigaba da aka samu a cikin kwanaki dari na farkon wa adin gwamnan na biyu.
Sunday bayan ya godewa Allah ma daukakin sarki ya kuma yaba da irin aiyukan cigaba da gwamnan yayi a farkon kwanaki dari da yayi akan Mulki Wanda Kuma ya taka rawan gani wajen kawo zaman lafiya dama inganta tsaro a fadin jahar baki daya.
Sunday yace ko a makon da ta gabatama gwamnan da yan majalisarsa sun amince da ware kudi da yakai Sama da nera bilyon daya domin magance matsalar ambaliyar ruwa a sashin anguwanin samunaka, Waru Jabbe da dai sauransu.
Ga Kuma yadda gwamnan ya kudiri aniyar tallafawa Al umma jahar da kayakin abinci taki da sauransu domin rage radadin wahala da aka shiga sakamokon cire tallafin maifetur Wanda gwamnatin tarayya tayi.
Ya Kuma kirayi kwamitin da gwamnan ya kafa domin rarraba kayakin tallafin da su gudanar da aiyukansu bilhakki da gaskiya domin ganin an samu nasaran rarraba kayakin yadda kamata. tare da Kiran jama da Suma suyi adalci Subaru wadanda basu dashi suje su karbi kayakin kada Wanda yake dashi Shima yaje ya karba.
Sunday Wugari ya shawarci Al ummar jahar da sukasance masu baiwa gwamnatin gwamna Fintiri hadin Kai da goyon baya domin ganin ya cimma burinsu na gudanar da aiyukan cigaban jahar ta Adamawa.
Dangane da aiyuka kuwa Sunday Wugari yace daman ai gwamnan ya dauko aiyukan cigaba Kuma zai Dora domin samun cigaban jahar ta Adamawa baki Daya.

Comments
Post a Comment