Kungiyar Yan Jarida a Najeriya N U J shiyar jahar Adamawa ta yaba tare da taya murna ga gwamnan Finti cika kwanaki dari a wa adinsa na biyu.
An yabawa gwamnatin jahar Adamawa karkashin jagotancin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa na mijin kokari da yayi wanjen gudanar da aiyukan cigaban jahar ta Adamawa a kwanaki dari da yayi bayan sake zaben da akayi a wa adin na biyu.
Kungiyar yan Jarida a Nijeriya N U J shiyar jahar Adamawa ne tayi wannan yabo a wata sanarwa da ta fitar a yola dauke dacsanya hanun sakatarenta Fidelis Jocthan.
Sanarwa ta baiyana cewa gwamnan ya gudanar da aiyukan cigaba sosai a cikin kwanaki dari da yayi akan mulki a wa adinsa na biyu, wanda kuma mutane sun amfana da shirye shiryen gwamnati daban daban.
Sanarwan ta yabawa gwamnan bisa yadda ya zabo kwamishinoninsa domin dorawa akan aiyukan da ya fara a wata adinsa na farko.
Kungiyar tace yan jahar Adamawa kamar sauran yan Najeriya ne suma sun dandanin radadin janye tallafi maifetur da akayi wanda hakan yayi sanadiyar hauhawan farashin kayakin masarufi dama na sifiri.
Wanda kuma gwamnan da dabarunsa ya dauki matakin sanarwa al umma dama ma aikataa jaha sauki inda ya sayo manyan motocin safa safa guda goma domin ganin ma aikata sunje wuraren aiyukansu cikin sauki da kuma suma Al ummar jahar sun samu saukin gudanar da zirga zirgansu cikin sauki daga ciki da wajen cikin garin Jimeta.
Bugu da karin gwamna Fintiri yayi abun azo a yaba inda ya karawa ma aikata dubu goma goma akan albashinsu wanda suka fara karba daga watan da ya gabata da kuma baiwa yan jahar buhun shinkafa mai nauyin kg 25 kyauta musammanma marassa galihu dake fadin jahar.
Kuma hatsima na kan hanya domin baiwa magidanta dake fadin jahar a yayinda aka samu zaman lafiya a dukkanin kananan hukumomin ashirin da daya. dake fadin jahar.
Duba da yadda irin wannan na mijin kokari da gwamna Fintiri yayi wajen tausayawa, da jinkain jama a da gwamnan yayi yasa kungiyar yan jarida wato N U J shiyar jahar Adamawa ta rubuta takardan yabo da kuma murnan cikan kwanaki dari da gwamnan yayi a wa a din na biyu a ofis.
Kungiyar ta N U J tana mai farin ciki da irin wadanan aiyuka kuma da fatan gwamnan zaicigaba da gudanar da aiyukan cigaban jahar musammanma wanzar da zaman lafiya a fadin jahar.
Rubuta takardan yabon dai ya biyo bayan amincewar shugaba kungiyar ta N U J a jahar Adamawa kwamuret Ishaka Donald Dedan da kuma membobin Kungiyar
.

Comments
Post a Comment