Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ya bankodo wani yunkurin yin garkuwa da wani.
A hobbasa da takeyi na dakile aikata yin harkuwa da mutane domin neman kudin fansa a fadin jahar Adamawa runduna yan sandan na jahar Adamawa ta takawa wasu masu yunkurin yin garkuwa da wani birki.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SPSuleiman Yahaya Ngurojene ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yola wanda kuma aka rabawa manema labarai.
Sanarwan ta baiyana cewa ofishin rundunan dake Karamar hukumar Gombe ne tare da hadin gwiwar sarkin bakan Gombi suka yi kokarin takawa wasu birkin yin garkuwa da wani mai suna Gideon Bitrus dake zaune a kauyen Jangra a karamar hukumar ta Gombi a jahar Adamawa.
Kakakin yace an samu nasaran hakane biyo bayan bayanain sirri da aka samu wanda hakan yasa hukumar yan sandan batayi da wasaba wajen kai dauki wurin da ake zargi mafakan masu garkuwa da mutanen ne. Inda kuwa akayi nasaran tarwatsasu harma an gano wasu kayaki da suka hada da karamin bindiga kiran gida, albarushe da dai sauransu.
Kwamiahinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya yabawa DPO dake ofishin yan sandan a karamar hukumar Gombi da Jami ansa da kuma mafarauta bisa kokarinsu da dakile aiyukan ta addanci a yankin baki daya.
Kwamiahinan ya kuma kirayi daukacin al ummar jahar da sukasance masu taimakawa rundunan yan sandan da wasu bayanai da zai baiwa rundunan damar kama wadanda ake zargi da aikata laifuka.
Ya kuma tabbatarwa gwamnati dama al ummar jahar Adamawa da cewa rundunan a shirye take ta kare rayuka dama dukiyoyin jama a baki daya.

Comments
Post a Comment