Yajin aikin gargadi na kwanann na biyu ya samu goyon bayan membobin kungiyar kwadigon a jahar Adamawa.
A yayinda aka shiga rana ta biyu a yajin aikinda kungiyar kwadigo a Najeriya keyi a matsayin na gargadi Kuma rana ta kashe membobin kungiyar damq ma aikatu sun bada hadin Kai da goyon baya dangane da yajin aikin.
Shugaban kungiyar kwadigo a Najeriya N L C shiyar jahar Adamawa kwamuret Emmanuel Fashe ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a yola dangane da yajin aikin game gari da kungiyar kwadigo keyi.
Emmanuel Fashe yace kawo yanzu membobin kungiyar sun amsa kira domin kuwa a yanzu haka wurare irinsu tahashi, ma aikatu, sakateriya, Bankuna suna rufe Wanda acewarsa yajin aikin na gargadin yayi tasiri kenan.
Ya Kuma shaidawa gwamnatin tarayya cewa bada sonsune suke shiga yajin aikiba Kuma bada sonsune suke yin zanga zangar lumanaba. Saboda haka yana mai Kiran gwamnati da tayi dukkanin abunda suka dace domin ganin ta biyawa ma aikatan bukatunsu.
A vwarsa dai in har gwamnati ta gaza wajen biyan bukatun maikatan to kartani da wai zasu sake shiga yajin aiki.
Yajin aikin gargadi da kungiyar kwadigon ta shiga na kwanaki biyun dai ya biyo bayan gaza cimma yar jejeniya da gwamnatin tarayya tayi da kungiyar kwadigon a kwanakin baya. Biyo bayan janye tallafin maifetur da shugaban kasa Bola Tinubu yayi. Wanda hakan ya sanya Al ummar da ke fadin kasar cikin tsadar rayuwa.

Comments
Post a Comment