Rundunan Tsaron Civil Defence tayi nasaran cika hanu da mutane takawa da ake zargi da satan shanu a jahar Adamawa.

A kokarinta na dakile aiyukan aikata laifuka Rundunan bada kariya ga fararen hula wato Civil Defence shiyar jahar Adamawa tare da hadin gwiwar Rundunan sojojin Najeriya sunyi nasaran kama wadanda ake zargi da satan shanu, wadanda suka addabi wasu sassan jahar ta Adamawa. Kakakin rundunan ta NSCDC a jahar Adamawa DSC Amidu Nyako Baba ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Sanarwan ta baiyana cewa eukunin farko na wadanda ake zargi da satan shanun an kama sune a gadan Numan wajen shingen binciken ababen hawa na sojoji wadanda suka hada da Dankadi Yakubu Mai shekaru 35, Samson James Dan shekaru 17, Usman Sule shekarunsa 30 da Kuma Usman Muhammed Mai shekaru 18 Kuma an kamasu da shanun ne a cikin wata mota Kiran Mai kujeru 18 Mai daike da rijistan numba SMK417AY Wanda Kuma an kama sune kan hanyarsu ta zuwa Gombe. an kuma gano makamai masu hatsari a wurinsu. Harwayau sanarwan ta Kara da cewa an sake kama wasu da ake za...