Hukumar kare haddura ta kasa FRSC Shiyar jahar Adamawan tace ta kimtsa tsaf domin dakile haddura a lokacin bikin Babban Sallah dake tafe.




Daga Alhassan Haladu Yola.



A yayinda aka fuskanci bikin Babban Sallar laiyya na shekara ta 2027, Hukumar kare haddura ta kasa tace ta kimtsa tsaf wajen daukan dukkanin matakai da suka dace domin ganin ba a Samu hadduraba a kafin, lokaci, dama bayan bukuwar Babbar Sallar.


Sector kwammandan Hukumar ta FRSC  a jahar Adamawa Ibrahim Abubakar Sadiq ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a Yola.


Sector Kwamanda Ibrahim Abubakar Sadiq yace sun dauki dukkanin matakai da suka dace domin tabbatar da ganin an kammala bukukuwar sallar lafiya, na tare da an Samu hadari ko asaran rayukaba.



Ibrahim Abubakar Sadiq ya Kara da cewa Hukumar tunin ta rarraba jami anta a dukkanin inda ake Samu cunkoson ababen hawa wadanda ke wurare daban daban dake fadin jahar, a Wani mataki na rage yawan cunkoson ababen a sassa daban daban dake fadin jahar.


Kwamanda Ibrahim Sadiq ya Kuma baiyana cewa Hukumar ta shirya  tsaf domin tunkaran bukukuwar sallar domin tabbatar da ganin an kula da lafiyar Al umma a lokacin bukukuwar sallar.




Kwamanda yace Hukumar ta dauki matakin wayarwa Al umma Kai a bangarori daban daban da suka hada da masallatai, mujami u, taahishin motoci da dai sauransu Wanda hakan zai taimaka wajen raguwar hadura akan hanyoyi dake fadin jahar dama kasa baki Daya.




A cewar kwammandan dai Hukumar tunin ta baza komarta a lunguna da Sako Sako domin Sanya Ido akan hanyoyi da Kuma yadda ake gudanar da harkokin tuki dama kula da lafiyar motaci yadda ya Kamata.



Abubakar Sadiq ya kirayi matuka ababen hawa da su Maida hankali wajen tukinsu, su Kuma tabbatar da cewa sun mallaki lasisi tuki Wanda hakan ne zai basu damar yin tuki na tare da matsalaba.



Ya kirayi iyaye da sukasance masu Hana yaransu yin gangamci da ababen hawa suka daina baiwa yaron da Bai mallaki hankalinsaba mota Wanda hakan zai saahi cikin matsala.



Yace iyaye suna da muhimmiyar rawa da zasu iya takawa wajen kula da Yara a lokacin bukukuwar sallar, saboda haka Yana da matukan muhimmanci iyaye sukasance masu Sanya Ido akan yaransu yadda ya Kamata.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.