NSCDC TA WARE JAMI ANTA 1352 DOMIN TABBATAR DA GANIN ANYI BUKUKUWAR SALLAR LAFIYA.
DAga Alhassan Haladu Yola.
Rundunan tsaro Bada kariya ga fararen hula a Najeriya Civil Defence Shiyar Jahar Adamawa ta lashi takwabin ganin ta inganta tsaro a lokacin bukukuwar Babban Sallar wannan shekara ta 2026 a dukkanin kananan hukumomi 21 dake fadin Jahar Adamawa.
Jami in hulda da jama a na rundunan a jahar Adamawa DSC Amidu Nyako Baba ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a Yola.
DSC Amidu Nyako Baba yace Rundunan ta Civil Defence karkashin jagorancin kwamanda Idris D Bande tunin ta tura jami anta 1352 domin tabbatar da Bada tsaro a dukkanin inda za a gudanar da Sallar Idi dama wuraren bukukuwar sallar a fadin jahar ta Adamawa.
DSC Nyako Baba yace Rundunan ta dauki dukkanin matakai da suka dace domin ganin ba a Samu matsalaba a lokacin bikin Babbar Sallar tare da shawartan Al umma da su kasance masu taimakawa Rundunan da wasu bayanain sirri, Wanda zai baiwa rundunan damar dakile duk wata barazana da zai iya kawo matsala a lokacin bukukuwar sallar.
Amidu Nyako ya Kuma tabbatar da cewa Rundunansu a shirye take ta baiwa Al umma kariya a Koda yaushe domin ganin a Samu wanzar da zaman lafiya a dukkanin kananan hukumomi 21 dake fadin jahar Adamawa.
A cewar Amidu Baba rundunan zata gudanar da sintiri a lunguna da Sako Sako dama wuraren taruwar jama a kamar tashan motoci da Kuma wurin da za a gudanar da sallar Idi da dai sauransu domin tabbatar da ganin an kammala bukukuwar sallar lafiya.
Baba ya Kuma kirayi daukacin Al ummar jahar Adamawa da su baiwa rundunan hadin Kai da goyon baya domin tabbatar da ganin komai ya tafi dai dai ba tare da wata matsalaba.
Ya kuma kirayi iyaye da Babbar murya wajen Sanya Ido akan yaransu da Kuma Maida hankali a kansu domin kaucewa shiga wata matsala a lokacin bukukuwar sallar.

Comments
Post a Comment