Babbar makarantar sakandaren gwamnati dake Hong tayi bikin yaye dalube karao na 55.
Daga Alhassan Haladu Yola.
Babban makarantar sakandaren Hong ta gudanar da bikin yaye dalubenta karo na 55 bikin Wanda ya Samu halartan Yan uwa da abokan arziki harma da tsoffin daluben makarantar dama shuwagabanin makarantu daban daban na ciki da wajen karamar Hukumar Hong dake jahar Adamawa.
Bikin yaye dalube ya gudana ne a harabar makarantar dake cikin karamar Hukumar Hong dake jahar Adamawa.
Da yake jawabi a wurin bikin Babban sakataren riko a Hukumar dake kula da makarantu sakandare a jahar Adamawa Mr Birsan Penuel ya nuna godiyarsa ga Allah Madaukakin sarki da ya bashi damar kasancewa a wurin bikin tare da yabawa Hukumar gudanarwar makarantar bisa shirya wannan biki mai tarihi da Kuma irin nasarori da aka Samu.
Mr Birsan Penuel ya Yaye da wadanda suka Samu kyaututtuka murna saboda jajircewarsu da sukayi. Tare da Kiran su da su cigaba da nuna halaye na gari da jakadu na gari domin zama abin alfahari a duk inda suke, harama da daga martanan jahar ta Adamawa.
Mr Penuel yace irin wannan nasarori da da aka Samu ba na mutum Daya bane na mutane da dama, saboda haka ya godewa daukacin malamai da ma sauran ma aikatan makarantar bisa hakuri da suka nuna da Kuma yin aiki tare.
Mr Birsan ya yabawa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa kokarinsa in inganta tare da bunkasa harkokin ilimi a fadin jahar Adamawa. Haka Kuma ya yabawa mataimakinyar gwamna Farfesa Kaletapwa G Farauta Wanda itama ta Bada gudumawa sosai wajen cigaban ilimi a fadin jahar.
Ya Kuma godewa kwamishinan ilimi tare da Babbar sakatariyar ma aikatan ilimin a jahar Adamawa bisa goyon baya da suka bayar wajen inganta ilimi a fadin jahar ta Adamawa.
Harwayau ya yabawa iyaye dangane da jajircewa da sukeyi wajen taimakawa malamai domin ganin an Samu nasaran inganta ilimi yadda ya Kamata.
A jawabinsa na maraba shugaban makarantar Babbar sakandaren gwamnati dake Hong Mr Yarima Emmanuel ya baiyana cewa wannan biki ya basu damar baiyana irin kokari da makarantar tayi na ganin an Samu damar baiwa Yara inganceccen ilimi ba tare da wata matsalaba.
Mr Yarima ya Yaya wadanda suka kammala makarantar murna tare da ciwa makarantar zata cigaba da yin dukkanin abinda suka dace domin cigaban aiyukan makarantar yadda ya Kamata.
Ya Kuma godewa dukkanin malamai dama sauran ma aikatan makarantar bisa yadda suka sadaukar da kansu wajen ganin makarantar ta Samu nasaran inganta ilimi a tsakanin dalube dake makarantar yadda ya dace.
Shima ya yabawa tsoffin daluben makarantar bisa irin rawa da suka dauka wajen cigaban makarantar Wanda acewarsa sun Bada gudumawa sosai wajen gudanar da harkokin makarantar ba tare da ganin an Samu matsalaba.ya yabawa iyaye inda yace Suma sun Bada gudumawa wajen tafiyar da harkokin makarantar.
Shugaban makarantar yace wannan shine karo na 55 da biyar kenan ake gudanar da irin wannan biki na yaye dalube a harabar makarantar.
Da yake nashi jawabi Omarana Suleiman Dan takaran kujeran gwamna na jam iyar ADC a jahar Adamawa. Wanda Kuma shine shugaban Taron ya yabawa makarantar bisa Shiyar wannan biki Wanda acewarsa Shima a makarantar yayi karatu, saboda haka a shirye yake ya gudanar da duk wasu aiyukan cigaban makarantar.
Ya shawarci shuwagabanin makarantar da su cigaba da gudanar da aiyukan makarantar yadda ya Kamata domin ganin an Samu cigaban ilimi a karamar Hukumar ta Hong dama jahar baki Daya.
Omarana Suleiman ya Kuma dauki nauyin karatun dalubar da tayi fice zuwa Jami a. Inda ya kirayi sauran dalube da su cigaba da Maida hankali wajen karatunsu yadda ya Kamata.
Masu gabatar da jawabi dai sun yabawa shugaban makarantar bisa kokarinsa na gudanar da kyakkawar shugabanci Wanda Kuma ya zama abin koyi don haka ya Bada gudumawa sosai wajen cigaban makarantar a karamar Hukumar ta Hong.
A yayin bikin an dai gudanar da kadai kadai da rawa rawen gargajiya da dai sauransu.

Comments
Post a Comment