MAKARANTAR SABILU RASHAD TAYI BIKIN YAYE DALUBE KARO NA SHA BIYU.






By Alhassan Haladu Yola.


Makarantar Sabilu Rashid dake Yola tayi bikin yaye dalubenta karo na Sha biyu Wanda bikin ya Samu halartan iyaye da Yan uwa da abokan arziki daga sassa daban daban daga cik da wajen karamar Hukumar Yola ta kudu dake jahar Adamawa.


Bikin dai ya gudanane a harabar makarantar dake cikin garin Yola a cikin karamar Hukumar Yola ta kudu..



Da yake jawabi Babban sakataren ilimin karamar Hukumar Yola ta kudu Wanda Kuma shine shugaban Taron Alh. Abba Yarima ya yabawa Wanda ta assasa makarantar ta Sabilu Rashada wato Hajiya Maryam Baba Lau Hassan, bisa kokarinsa na assasa wannan makarantar. Wanda a cewarsa hakan ya bunkasa harkokin ilimi a tsakanin Yara dake ciki da wajen karamar Hukumar Yola.



Ya Kuma jinjinawa shugaban makarantar da malamai bisa jajircewarsu domin tabbatar da ganin yaran sun Samu inganceccen ilimi yadda ya Kamata.



Abba Yarima ya tabbatar da goyon bayansa dangane da yadda ake tafiyar da harkokin karantarwar makarantar Wanda a cewarsa hakan ya taimaka sosai wajen cigaba dama inganta karatun makarantar. Don haka nema yake Kira ga iyaye da su baiwa makarantar ta Sabilu Rashad hadin Kai da goyon baya domin Samun cigaba ilimi.



Hakimin Yola Kuma Daukan Adamawa, Alh. Zubairu Adamu Shima yabawa yayi da yadda makarantar Sabilu Rashad ta dukufa wajen baiwa Yara tarbiya da Kuma Basu inganceccen ilimi da suka hada da na addini harma Dana zamani, Wanda a cewarsa hakan cikagabane matuka.

 


Hakimin ya Kuma tabbatar da goyon bayansa da makarantar ta Sabilu Rashad tare da Kiran dalube musammanma wadanda aka yaye da suyi amfani da ilimi da suka Samu domin Samun cigaban ilimi su yadda ya Kamata.




Shugaban karamar Hukumar Yola ta kudu Barr. Babaiyal Wanda Dr Abdullahi Muhammed ya wakiltar Shima jaddada goyon bayansa yayi da bikin yaye dalube da karantar Sabilu Rashad ta Shiyar inda yace wannan abun yabawa ne Kuma zaikawo cigaba yadda ya Kamata.



Ya Kuma shawarci daluben musammanma wadanda aka yaye da su cigaba da karatunsu zuwa makarantu na gaba domin Samun cigaban ilimi da suka Samu kana sukasance masu Nuna da a ga shuwagabanin su, tare da Kiran iyaye da Suma su Bada masu gudumawar wajen baiwa makarantar hadin Kai da goyon baya domin ganin makarantar ta Samu nasaran Bada inganceccen karatu ga Yara.



Hajiya maisaratu Bello ta yabawa daluben bisa jajircewarsu da Kuma juriya da suka Nuna a lokacinda suke karatu, saboda haka su Kara juriya da Kuma cigaba da karatu domin ganin sun Samu nasara a rayuwarsu.




Ta Kuma shawarci yaran da suke cikin da Suma sucigaba da karatunsu da Kuma Nuna da a da biyayya ga shuwagabanin makarantar domin Samun albarkan karatunsu yadda ya Kamata.



Itama da take nata jawabi Hajiya Mariya Nyako ta Nuna Jin dadinta dangane da wannan biki Wanda acewarsa Bata tana ganin irin wannan biki na yaye dalube a makarantar kamar wannanba.



Ta Kuma yabawa Wanda ta assasa makarantar bisa wannan kokari da tayi domin hakan ya kawo cigaba matuka. Itama ta shawarci iyaye da su baiwa makarantar hadin Kai da goyon baya domin ganin an Samu cigaba yadda ya Kamata.



Hajiya Maryam Baba Lau Hassan Wanda itace ta assasa makarantar da baiyana cewa bikin na bana yafi na bara saboda yadda iyaye da dalube suka baiwa bikin muhimmanci. Ta Kuma tabbatar da cewa zatayi dukkanin maiyiwa domin inganta karatun makarantar a dukkanin bangaren.




Da yake jawabin godiya Alh. Gidado Muhammed Hassan ya godewa Hakimin Yola, shugaban karamar Hukumar Yola, maijimillar bole, dam dukkanin wadanda suka jalaci bikin daga ciki da wajen karamar Hukumar Yola ta kudu.


Akalla dalube 57 ne aka yaye a bana wato shekara ta 2026, daga makarantar na Sabilu Rashada.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie