AN SHAWARCI AL UMMA MISULMAI DA SU SANYAWA YARANSU SON MANZON ALLAH TUN SUNA YARA DOMIN CIGABAN ADDININ MUSULUNCI.



Daga Alhassan Haladu Yola.


An shawarci iyaye musammanma mata da sukasance masu koyawa yaransu son manzon Allah da iyalensa tun suna Yara domin hakan zai taimaka wajen inganta rayuwarsu yadda ya Kamata.


Hajiya Amina Muhammed Bashir ne ta Bada wannan shawara a lokacin da take jawabi a wurin bikin Maulidi Manzon Allah da aka gudanar a gidan Modibbo Ahmadu Ganye dake cikin karamar Hukumar Ganye a jahar Adamawa.


Hajiya Amina tace Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace ku koyawa yaranku abubuwa uku Son Allah, son Annabi, da iyalen gidansa don haka ya Kamata iyaye su Kara himma wajen nunawa yaransu son Annabi da Kuma Yi masa biyayya.


Ta Kuma kirayi wadanda suka halarci bikin na maulidi da sukasance suna amfani da abinda sukaji ma nasihohi da aka gudanar a waurin bikin. Domin Samun cigaba addinin musulunci yadda ya Kamata.


Ta Kuma shawarci mahalarta bikin da sukasance jakatu wajen isar da duk bayanai da sukaji ga sauran Al umma da Basu Samu damar hakartar bikin maulidi ba domin ganin nasihoh da aka gudanar ya Isa ga kowa.


Da take jawabi dangane da yadda bikin ya gudana a wannan shekara kuwa. Hajiya Amina tace bikin ya gudana cikin lumana Kuma yafi na sauran shekaru da suka gabata.


A cewarta bikin sai cigaba yake Yi a kowace shekara Wanda Kuma an dauki tsawon shekaru ana gudanar da bikin maulidi a gidan Modibbo Ahmadu Ganye.


Itama anata jawabi Barista Hapsat Usman ta yaba da yadda bikin Maulidi ya gudana domin a cewarta bikin ya Bada Sha awa sosai musammanma yadda aka Samu halarta Yara da iyayensu.


Barista Hapsat ta yabawa wadanda suka shirya wannan biki na Maulidi karkashin jagorancin Hajiya Amina Muhammed Bashir tare da Kiran wadanda suka halarci bikin da suyi aiki da abin da sukaji domin Samun nasara a rayuwarsu yadda ya Kamata.


Malamai da dama dai sun gudanar da jawabai da nasihohi a wurin bikin na Maulidi dama gudanar da Adu o I na musamman domin Neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubale tsaro a fadin Najeriya dama saukinbrayuwa.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie