An shawarci musulmai da kiristoci da sukasance masu hada kansu domin Samar da zaman lafiya mai daurewa.





Daga Alhassan Haladu Yola.



 Gabannin Babban zaben shekara ta 2027 an kirayi mabiya addin musulunci da mabiya addinin kirista da sukasance masu hada kansu wajen guda tare dayin dukkanin abinda zaikawo hadin Kai da cigaba a tsakanin Al umma baki Daya.


Kiran na zuwa ne a yayinda majalisar addinin musulunci na jahar Adamawa tare da kungiyar kiristoci a Najeriya CAN Shiyar jahar Adamawa karkashin majalisar dake shiga tsakini addinai a Najeriya NIREC. suka fara ziyarantar kananan hukumomin dake fadin jahar da zummar wayarwa mabiya addinain biyu Kai dangane da mahimmancin zaman lafiya.dama hadin Kai.



An dai fara ziyaran ne da karamar Hukumar Mayo Belwa, da yake jawabi a wurin Taron shugaban majalisar addinin musulunci a jahar Adamawa Kuma shugaban majalisar dake shiga tsakanin addinai a Najeriya NIREC. Alhaji Gambo Jika yace makasudin fara wannan ziyaran dai itace ganawa da mabiya addinain biyu domin zakulo janyoyin da za Abi domin magance dukkanin banbance banbance da ake Samu a tsakanin addinain biyu, domin Samar da zaman lafiya mai daurewa a jahar dama kasa baki Daya.



Alhaji Gambo Jika ya Kuma kirayi mabiya addinain biyu da sukasance masu hada kansu da Kuma yin aiki tare a Koda yaushe Wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen zama tsintsiya madaurinki Daya, tare Kuma da Jan hankalin su da kada su bari ayi amfani da su  wajen  Raba kan Al umma.



Jika ya Kara da cewa Yanzu  an fuskanci Babban zaben shekara ta 2027 don haka sukasance masu taka tsantsan da Yan siyasa  a yayin gangamin Neman zabe, inda ya shawarci Al umma da kada  ayi amfani da su wajen Raba kan jama a da sunan siyasa.



Ya Kuma kirayi Yan siyasa da sukasance masu gudanar da gangamin Neman zabe su bisa tsari na tare da kawo abinda zai Raba kan Al umma ba, domin Samun zaman lafiya da Kuma cigaba.



Shima anashi jawabi shugaban kungiyar kiristoci a Najeriya CAN Shiyar jahar Adamawa kana shugaban majalisar dake shiga tsanin addinai a Najeriya NIREC. Dr Rev. Joel Manzo yace Allah madaukakin sarki shi halalci duk Wani Dan Adam don haka baiga dakilin da yasa ake Samu banbance banbance a tsakanin jama a ba, domin a cewarsa dole ne a zauna tare a rayu tare saboda haka Al umma suyi karatun ta nitsu domin kaucewa dukkanin abinda zaikawo matsalar a tsakanin Al ummah.



Dr Rev. Joel Manzo ya jadda kiransa ga mabiya addinain biyu da cewa su sanifa duk Wani Dan siyasa da da zaiyi amfani da addini ko kabikanci to zai tafi ya barsu tare, don haka Al umma sukasance masu fahintar Juna, da nunawa Juna kauna da mutunta Juna, a Koda yaushe Wanda hakan zai taimaka wajen Samar da hadin Kai da cigaba yadda ya Kamata.



Rev. Joel Danjuma Manzo ya kirayi shuwagabanin addinain biyu dake kananan hukumomin  da sukasance masu yin aiki tare da Kuma tattaunawa domin warware dukkanin matsaloli da ake fuskanta a tsakanin Al ummah.



Wasu daga cikin mabiya addinain biyu dai sun Nuna farin cikinsu dangane da irin wannan wayar musu da Kai da akayi Kuma za suyi amfani da abinda sukaji domin Samun cigaba.



Kungiyar ta NIREC ta ziyarci kananan hukumomin Mayo Belwa, Jada, Ganye, da Kuma karamar Hukumar Tongo dake fadin jahar Adamawa.

Comments

Popular posts from this blog

π€πƒπ€πŒπ€π–π€ ππŽπ‹πˆπ‚π„ π‚πŽππ…πˆπ‘πŒ 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR π€π‚π‚πˆπƒπ„ππ“ πˆππ•πŽπ‹π•πˆππ† πŒπˆπ‹πˆπ“π€π‘π˜ π•π„π‡πˆπ‚π‹π„ 𝐀𝐍𝐃 π‚πŽπŒπŒπ„π‘π‚πˆπ€π‹ 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie