Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta shiyar B tace tayi nasaran kama mutane akalla dari tara da saba in da bakwai a shekara ta 2022.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya N D L E A shiyar B Wanda ya kunshi jihohi Adamawa, Taraba da kuma jahar Gombe tace tayi nasaran kama mutane dari Tara da saba in da bakwai wadanda ake zargi da safaran miyagun kwayoyi a Yankin na B. Kwamadan hukumar a yankin na B Alhaji Idris Bello ne ya baiyana haka a lokacin da yake Zantawa da jaridar Al Nur a yola, dangane da irin nasarorinda hukumar ta N D L E A tayi a shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu a yankin. Kwamandan yace cikin wadanda aka kama dari tara da saba in da bakwai wadanda suka hada da mata an yankewa dari uku da sittin da biyar hukunci a yayinda dari uku da saba in da hudu kuma an basu shawarwari domin su daina ta ammali da miyagun kwayoyin. Alhaji Idris Bello ya kuma baiyana cewa hukumar tayi nasaran kama miyagun kwayoyi da nauyinsa yakai kilo grama milyon biyu da dubu dari bakwai da hamsin da bakwai da dari tara da saba in da uku. Wato 2,757,973. Da wannan ne kwamandan ya kirayi al umma da sukasance masu taimakawa hukumar da duk wasu bayanai da zai baiwa hukumar damar dakile safara dama ta ammali da miyagun kwayoyi. Ya kuma shawarci iyaye dama shuwagabannin Al ummah da su bada tasu gudumawa wajen dakile sha da fataucin miyagun kwayoyi a tsakanin al umma domin samar da zaman lafiya dama cigaban kasa baki daya. Ya kuma kirayi matasa da su nisanta kansu daga ta ammali da miyagun kwayoyi domin suma su bada tasu gudumawa wajen wanzar da zaman lafiya dama cigaban kasa.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.