An bukaci hadin Kai a tsakanin shuwagabanin da wadanda ake mulka domin magance matsalar cin hanci da rashawa.

An bukaci kyakkawar gwamnatin da adalci domin kawar da matsalar cin hanci da rashawa a tsakanin Al umma. Farfesa Abdullahi Bashir ya baiyana haka a lokacin da yake gabatar da lekca a wurin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki Wanda kungiyar wadata Media Advacacy tare da hadin gwiwar Fombina FM suka shirya a yola. Farfesa Abdullahi Bashir yace Yana da muhimmanci gwamnati ta maida hankali wajen yin adalci da kyautatawa jama a a wani mataki na magance matsalar cin hanci da rashawa dama Samar da zaman lafiya. Yace Babban matsalar da ake samu a yanzu shine rashin fahintar Juna a tsakanin gwamnati da wadanda ake mulka don haka akwai bukatar gwamnatin tayi dukkanin maiyiwa domin inganta aiyukanta ga Al umma Wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen rage radadin cin hancin a tsakanin Al umma. Tunda farko a jawabinsa Malam Zubairu Idris AbdulRa uf yace rashin kyakkawar shugabancinse da wasu keyi yasa ake fuskantar matsΓ lolin da dama ciki harda cin hanci da rashawa Malam Zubairu yace ya kamata a bulo da dabaru da zasu taimaka wajen yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin jama a dama shirya tarurruka na wayarwa Al umma Kai dangane da matsalar ta cin hanci da rashawa. Shima a jawabinsa wakilin kwamishinan hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa dama lafuka dake da halaka da cin hanci Mr Benjamin Francis Wanda Kuma shine Jami in watsa labarai hukumar a jahar Adamawa yace ya kamata a samu kyakkawar halaka a tsakanin gwamnati da sauran Al umma ta wayar musu da Kai da Kuma basu bayanai na gaskiya A jawabinsa na godiya Babban manajan gidan rediyo Fombina FM yola Alhaji Dahiru Garba Muhammed yace Yana da muhimmanci mutane su bukaci gaskiya da adalci. Ya Kuma yabawa kungiyar ta WAMAC bisa shirya wannan taro tare da baiyana aniyarsa na hada Kai domin samun nasaran yakan cin hanci da rashawa. Da yake nashi jawabi Alhaji Usman Ahmed Dadah Wanda shinema ya wakilcii Hakimin Jimeta ya baiyana cewa sarakunan gargajiyΓ  suna da rawa da zasu iya takawa wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Comments

Popular posts from this blog

π€πƒπ€πŒπ€π–π€ ππŽπ‹πˆπ‚π„ π‚πŽππ…πˆπ‘πŒ 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR π€π‚π‚πˆπƒπ„ππ“ πˆππ•πŽπ‹π•πˆππ† πŒπˆπ‹πˆπ“π€π‘π˜ π•π„π‡πˆπ‚π‹π„ 𝐀𝐍𝐃 π‚πŽπŒπŒπ„π‘π‚πˆπ€π‹ 𝐁𝐔𝐒

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

TETFund Director Commends MAUTH Doctors Over Successful Separation of Conjoined Twins