An rantsar da sabbin shuwagabanin kungiyar Yan kasuwa a jahar yobe
Daga Ado Yaro Gashuwa Damaturu.
Hadakar kungiyoyin yan kasuwa dake jahar Yobe sun gudanar da zaben sabbin shuwagabanin kungiyar wadanda zasuja ragamar kungiyar na shekaru hudu masu zuwa.
An dai gudanar da zabenne a Dakin taro dake cikin garin Damaturu fadar gwamnatin jahar Yobe.
Da yake jawabi a lokacin zaben shuhaban kwamitin shirya zaben Alhaji Ibrahim Muhammed Bello ya kirayi membobin kungiyar da sukasance masuyin aiki tukuru domin cigaban kungiyar a fadin jahar baki daya.
Alhaji Ibrahim Muhammed Bello ya yabawa membobin kungiyar bisa hadin kai da suka bayar a wajen zaben wanda hakan yasa aka gudanar da inganceccen zaben. Kuma yayi amfani da wannan damar domin yabawa gwamnatin Mai Mala Buni bisa kokarinta na baiwa kungiyar hadin kai harma da taimakawa kungiyar dama yan kasuwa dake fadin jahar.
Wadanda aka zaban dai sun hada da Alhaji Muhammed Muktar Kime a matsyin shugaba, sai Ibrahim Ahmed Adam a matsayin mataimakin shugaba, da Abubakar Audu Agwai a matsayin sakatare, sai kuma Goni Ngoma Garba mataimakin sakatare, Alhaji Buba Umar mai goro, Bukar Muhammed Bk sakataren kudi, da kuma Muhammed Sani Auwal mai bincike a yayinda Hajiya Hadiza Lawan zata kasance shugaba mata sai kuma Alhaji Ado Yaro Gashuwa a matsayin P R O.
Sauran sun hada da Alhaji Muhammed Dallatu ya zama shugaban yankin A da Alhaji Bello Dumbuwa zai kasance shugaban yankin B da kuma Alhaji Tanko Hamza shugaban yankin C.
Da yake jawabin amincewa sabon zabebben shugaba kungiyar Alhaji Muhammed Muktari Kime ya tabbatar da cewa zaiyi aiki kafada da kafada da membobin kungiyar domin samun cigaban kungiyar tasu. Ya kuma tabbatar da cewa kofarsu a bude wajen karban shawarwarin da zai kawo cigaban kungiyar.
Alhaji Muhammed Muktari Kime ya kirayi membobin kungiyar da sukasance suna baiwa shuwagabanin kungiyar hadin kai da goyon baya domin ganin kungiyar da samu cigaba yadda ya kamata.
Yace bari yayi amfani da wannan damar wajen godewa tare da yabawa gwamnatin mai Mala Buni bisa na mijin kokari da gwamnatin tayi na gyara kasuwani biyar a fadin jahar. Wanda kuma hakan ya sa aka samu cigaban harkokin kasuwanci a fadin jahar baki daya.






Comments
Post a Comment