An yabawa masuyiwa kasa hidima a jahar Taraba.
Daga Sani Yarima Jalingo.
Gwamnan jahar Taraba Dr Agbu Kefas ya yabawa masuyiwa kasa hidima bisa kokarinsu na kirkiro tare da koyon sana o in dogaro da Kai karkashin shirin nan na koyar da kananan sana o I da cigaba wato (SAED).
Dr Àgbu Kefas ya baiyana haka ne a wajen bikin Bude wayarwa masuyiwa kasa hidima Kai na shekara ta dubu biyu da ashirin da uku na rukunin A Wanda aka gudanar a sansanin masuyiwa kasa hidima na dindindin dake Sibre, a karamar hukumar Ardo Kola dake jahar Taraba.
Gwamnan Wanda kwamishinan cigaban matasa da wasanni Ambasada Joseph Joshua ya wakilta yace masuyiwa kasa hidima sunyi rawan gani Kuma abun a yabane saboda sun samarwa kansu aiyukan da zasu dogara da kansu.
Ya Kuma kirayesu da sukasance masu kyakkawar dabi a da Kuma bin doka da oda a Koda yaushe tare da yin tsare tsaren da zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki a fadin jahar baki Daya.
Ya Kuma tabbatar da cewa gwamnatin zatayi dukkanin maiyiwa domin inganta tsaro dama kula da walwalan masuyiwa kasa hidima a jahar. Domin samun damar inganta aiyukansu.
Shima a jawabinsa Babban sakatare a ma aikatar harkokin matasa da wasanni Wanda kwamishinan ya wakilta ya godewa gwamnan bisa halartan bikin tare da godewa masuyiwa kasa hidima bisa amincewa da sukayi na zuwa jahar Taraba domin yiwa kasa hidima .
Tunda farko a jawabinsa ko odinatan hukumar masuyiwa kasa hidima wato NYSC a jahar Taraba Mr Anthony Nzoka ya baiyana Jin dadinsa ga wakilin gwamnan dama Al ummar jahar Taraba bisa hadin Kai da goyon baya da suke baiwa masuyiwa kasa hidima a fadin jahar.
Ya Kuma shawarci masuyiwa kasa hidima da sukasance jakadu na gari tare da gudanar da aiyukansu yadda ya kamata.
Wakilin Babban alkalin jahar Mai sharia D. N Buba ne ya jagoranci rantsar da masuyiwa kasa hidima.




Comments
Post a Comment