Duba da yanayi na matsalar rayuwa da ake ciki anshawarvi Al umma da su maida lamuransu ga Allah Madaukakin Sarki.

An shawarc al umma da su maida dukkanin lamuransu ga Allah madaukakin sarki domin neman saukin rayuwa duba da yanayin tsadar rayuwa da ake ciki a yanzu biyo bayan cire tallafin maifetur wanda shugaban kasa Bola Tinubu yayi. Shugaban majalisar harkokin addinin musulunci a jahar Adamawa Alhaji Gambo Jika ne ya bada wannan shawara a zantawarsa da manema labarai a yola. Alhaji Gambo Jika yace yakamata da zaran an shiga wani yanayi da tsadar rayuwa to kamatayayi a maida hankali wajen yin adu o i da gudanar da aiyukan Alheri dimin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen wahalar rayuwa da ake ciki a halin yanzu. Ya kuma kirayi gwamnati da itama ta yi dukkanin abunda suka dace domin ganin ta tallafawa al umma saboda suma su samu saukin rayuwa kasancewa itace uwa mabada mama. Don haka ya kamata gwamnatin tarayya dana jahar da su tashi tsaye wajen tallafawa jama a biyo bayan yanayin matsin rayuwa da talakokin kasan nan suka shiga. Alhaji Gambo Jika ya shawarci yan kasuwa da suma sukasance masu tausayawa al umma a dukkanin kasuwancinsu domin suma su samu cigaban mai daurewa. Inda ya kirayi yan kaauwa da su sausauto da farashin kayakin masarufi duk dacewa anayin kasuwa don riba amman su kasance masuyin sauki a dukkanin lamuransu. A karshe yayi adu ar Allah madaukakin sarki ya kawo karshen matsalar baki daya da kuma samar da zaman lafiya mai daurewa a jaha dama kasa baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

TETFund Director Commends MAUTH Doctors Over Successful Separation of Conjoined Twins