Gwamnatin jahar Adamawa ta kafa kwamitin da kula da rarraba kayakin tallafi was Al ummar jahar ta Adamawa.

Gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Finti ya kafa kwamiti Mai mutane ashirin Wanda zai kula tare da rarraba kayakin tallafi domin ragewa Al ummar jahar radadin wahala da aka shiga sakamokon cire tallafin maifetur. Gwamna Ahmadu Umaru Finti ya baiyana haka ne a cikin wata sanarwa daga sakataren watsa labarain gwamnan Humwashi Wonosikiu da ya fitar Wanda aka rabawa manema labarai a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Kwamitin dai sun hada kungiyoyi, hukumomi,dama daidaikum jama a Wanda sune zasu kula da Kuma rarraba kayakin tallafin wa Al ummar jahar.
Acewar sanarwan dai karon farko za a rarraba kayakin abinci da suka hada da hatsi. Kuma a ranan Alamis 24-8-2923 ne za rantsar da kwamitin da misalin karfe goma sha Daya na safe a dakin taro na gidan gwamnati dake nan yola. Wanda Kuma sakataren gwamnatin jahar ta Adamawa. Awwal D Tukur zai kasance shugaban kwamitin.
Membobin kwamitin sun hada da sarkin Shelleng wato Amna Shelleng, sai hamma Bachama da mutane biyu daga majalisar dokokin kasa, da Kuma mutane biyu daga majalisar dokokin jaha,tare da kwamishinana dama shugaban ma aikatan jahar , shugaban ALGON, Brigade kwamanda, kwamishinan Yan sanda, Kwamandan sojojin Sama. Sauran sun hada da darektan hukumar tsaron farin kaya D S S, Kwamandan rundunan Civil defence, wakilin kungiyar CAN, da wakilin majalisar Addinin musulunci, wakilin kungiyar yan jarida NUJ, Dana kungiyar kwadigo NLC, sai na TUC, da Kuma na ADSEM.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

TETFund Director Commends MAUTH Doctors Over Successful Separation of Conjoined Twins