Gwamnatin jahar Yobe ta lashi takwabin inganta tsaro a fadin jahar.
Gwamnan jahar Yobe Mai Mala Buni yace gwamnatinsa zata cigaba da baiwa bangaren tsaro da ma walwalan masuyiwa kasa hidima musammanma wadanda aka turo hajar muhimmanci domin samun cigaba.
Gwamna Mai Mala Buni ya baiyana haka ne a wurin bikin tantsar da masuyiwa kasa hidima wato Rukunin B na shekara ta dubu biyu da ashirin da uku Wanda bikin ya gudana a sansanin masuyiwa kasa hidima dake Dazigau a karamar hukumar Nangere a jahar ta Yobe.
Gwamnan wanda mai taimaka masa na musamman aka koyar da sana o i da samar da aikikyi Abdullahi Bego ya wakilta ya baiyana cewa tunin aka umurci hukumomin tsaro da shuwagabanin al umma su tabbatar da ingancin muhallin masuyiwa kasa hidima.
Ya kuma kirayi masuyiwa kasa hidima da sukasance masu gudanar da aiyukansu yadda ya kamata domin samun cigaban sansanin.
Tunda farko a jawabinta ko odinaton hukumar masuyiwa kasa hidima a jahar Yobe Hajiya Hafsat Yarima ta baiyana cewa an dauki tsawon makwanni uku an horas da masuyiwa kasa hidima a fannoni daban daban harma da kananan sana o i.
Ta kuma yabawa gwamnatin jahar Yobe bisa hadin kai da goyon baya da take baiwa tsarin na masuyiwa kasa hidima a fadin jahar.
Wasu daga cikin masuyiwa kasa hidima sun baiyana farin cikinsu da gamsuwarsu dangane da haro da akayi musu.
Masuyiwa kasa hidima da yawansu ya kai dubu daya da dari biyu ne dai aka turo jahar ta Yobe.




Comments
Post a Comment