Sama da mutane dubu ashirin nedai zasu samu tallafi wadanda ambaliyar ruwan bara ya shafa a jahar Yobe.
A kalla mutane dubu ashirin da biyar wadanda ambaliyar ruwar bara ya shafa zasu amfana da tallafi daga gwamnatin tarayya a jahar Yobe.
Da yake kaddamar da rabon kayakin a gidan gwamnati dake Damaturu. Gwamna Mai Mala Buni yace jahar Yobe tana daya daga cikin jihohi da suka dan dana kudarsu a nangaren ambaliyar ruwa lamarin da yayi sanadiya mutuwar mutane sama da saba in.
Hukumar agajin gaggawa ta kasa NEMA tace tana iya kokarinta domin ganin an tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ya shafa a fadin kasar tun daga shekara ta 2022. domin ganin an cike gibin da aka rasa sakamokok ambaliyar ruwan a fadin Najeriya.
Gwamnan yace sama da magidanta arba in ne lamarin ya shafa tare da lalata hanyoyi da dama.
Gwamna Mai Mala ya yabawa gwamnatin ta tarayya bisa taimakon da tayiwa ambaliyar ruwa ya shafa a jahar ta kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa a shirye take ta cigaba da yin dukkanin abunda suka dace domin cigaban jahar.
Shima Babban darektan hukumar agajin gaggawa ta kasa NEMA Ahmed Mustafa wanda Hajiya Bintu Aliyu ta wakilta tace a karon farko mutane dubu tara ne suka amfana da taimakon a jahar Yobe.
Tunda farko a jawabinsa Babban sakateren hukumar agajin gaggawa a jahar Yobe Muhammed Goje ya baiyana cewa hukumar ta inganta aiyukanta domin ganin an taimakawa al umma yadda ya kamata.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin sun baiyana farin cikinsu tare da yabawa gwamnatin tarayya bisa wannan tallafi da akayi musu tare da yin al kawarin yin amfani da abida aka basu yadda ya kamata.
Kayakin da aka rarraban dai sun hada da kayakin noma, da injunan nika da dai sauransu.

Comments
Post a Comment