An kirayi manoma a jahar Adamawa da sukasance suna noma Alkama wanda hakan zaitaimakawa wajen samar da aikinyi a fadin jaha.
An shawarci manoma a jahar Adamawa da su fadada aiyukansu wajen noma alkama domin Samar da aiyukanyi a tsakanin matasa dake fadin jahar Adamawa.
Mai baiwa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jahar Adamawa shawara ta musamman akan harkokin noma da kananan sana o i Alhaji Usman Abubajar wanda akafi sani da Manu Ngurore ne ya baiyana haka a ganawarsa da manema labarai a yola.
Usman Abubakar yace noman alkama yana da mutukan muhimmanci wanda mutane da dama zasu amfana da shi don haka ya kamata manoma sukasance masu neman ilimin noman alkama domin bunkasa tattalin Arziki dama cigaban jahar.
Alhaji Usman ya kuma kirayi matasa da suma su shiga a dama dasu wajen noma alkama domin suma su bada tasu gudumawa wajen cigaban jahar.
Ya kuma kirayi gwamnati tarayya dana jahar da sukasance suna taimakawa manoman alkama a koda yaushe da kayakin aiki wanda aceqarsa hakan zai taimaka musu wajen gudanar da aiyukansu yadda ya kamata.
Kawo yanzu dai an kaddamar da shirin noman Alkama a wasu kanananan hukumomi dake fadin jahar Adamawa.

Comments
Post a Comment