Rundunan yan sanda a jahar Adamawa tayi nasaran tarwatsa maboyar masu aikata laifuka a jahar.

A kokarinta na dakile aikata ta addanci a fadin jaha rundunan yan sanda jahar Adamawa ta rundunanta dake yaki da aikata laifuka a wasu bangaren jihohin Taraba, Adamawa, Gombe, Yobe, da kuma jahuriyar Kamaru tayi nasaran dakile aiyukan bata gari tare da hadin gwiwar mafarauta. Kakakin rundunan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne dai ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar aka rabawa manema labarai a Yola. Haka kuma rundunan ta samu nasaran kawar da aiyuka masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, fashi da makami, barayin shanu dama dukkanin haramcecen aiyuka akan iyakokin ta Najeriya. Wadanda ake zargin masuyin garkuwa da mutanene da suka ga alamar Jami an tsaro wanda hakan yasa suka ranta ana kare inda aka bude musu wuta wanda hakan yasa wasu suka gudu da raunikan harbi a jikinsu. Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya baiyana farin cikinsa tare da jin dadinsa dangane da aiyukan da kwamandan sashin dake yaki da masu aikata laifuka wato Crack Squad tare da Jami an sa dama mafarauta saboda a cewar kwamishinan sun taka rawan gani wajen jajircewa wajen kare rayuka dama dukiyoyin Al umma. Kwamishinan ya kuma kirayi daukacin Al ummar jahar Adamawa da sukasance suna taimakawa rundunan yan sandan da wasu bayanai a koda yaushe domin samun nasaran kawarda aikata laifuka.musammanma da zaran sunga wadanda suka gudu da raunikan harbi a jikinsu. Harwayau kwamishinan ya tabbatarwa gwamnatin jaha dama Al ummar jahar cewa rundunan zata cigaba dayin dukkanin abinda suka dace domin tarwatsa maboyar masu aikata laifuka a fadin jahar ta Adamawa. Rundunan ta kuma gano bindigogi kiran AK 47 guda hudu dama arbarushe da dama.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.