An shawarci gwamna Fintiri dangane da raba tallafi.



Daga Ibrahim Abubakar Yola.

Mai Girma Gwamna Shawarar sun kasu Gida Hudu zuwa Biyar Amma Yau zan kawo Guda Daya Kawai sai wani sati zan Kara kawo na biyu


JIgo a siyasar jahar Adamawa Muhammed Ahmed Marafa Wanda ke unguwar karewar  ne ya bada wannan shawara a wata sanarwa da ya fitar a yola.


NA FARKO:

A) Idan kana da Niyan taimakawa da abincin Azumi, toh kayi kafin daukan Azumi ko Kuma a satin da za'a fara Azumi don WALLAHI dewa ma kwana da yunwa Kuma barai Yi Dadi wadda ya yini Yana Ibada Kuma ya Rasa Mai zai ci da Yamma ba


B) In ka tashi Rabiyar abincin, kayi Committee unguwa by unguwa sai a Dauki data na ko wani gida da yawan mutane da ke ciki don kaiwa kowa har kofar Gidan sa, wannan kadai zai Iya rage Almundahana cikin Rabiyar. Committee da zasu Yi aikin nan ya kasance akwai Mai Jimilla, Mai Unguwa, Limamai, APC/PDP Representatives na unguwa, Muslim Council Representative na unguwa, JNI/JIBWIS Representative na unguwa and Youth Representative na Unguwa. A jah musu kunne da cewa su ma kowa ya dauka dai mutanen da ke Gidan su ba suyi handama don sune Committee ba.


C) karkashin lura na mutanen nan da na irga a sama, zai Yi kyau ka Dauki shawarar da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da ya bawa Gwamnatin Kano da ana dafa abinci ko wani unguwa don wadatar da ciyawar a sakanin Al'umma.


4) Gaba Daya Adamawa Muna da ward 226, idan kayi multiplying by 3, zaka samu trailer 678 na abinci. Sai Mai Girma Gwamna ya saya set na trailer uku; set na Daya trailer Shinkafa 226, set na biyu trailer Maiwa da Gero 226, set na uku trailer Maggi, Oil, palm oil 226. Ko wani ward sai a Basu trailer 3 suje su Kasa karkashin surpervision na Hakimi, Mai Jimillu, Police Station, Muslim Council, Army da Councilor ward nasu. Wannan bashi zai Basu dama su debi kasu na kayan na daban ba, su ma za'a Basu deidei iya Gidan su.


5) Mai Girma Gwamna Matsalan da muke ciki a yanzun yunwa ne Kawai ke damun Al'umma, Kuma Rabiyar abincin nan zai shiga Gidan Musulmi, Christa harda wadda Bai da Addini. Zaka samu Lada, Kuma a cikin Wannan matsi na Rayuwa, zaka samu acceptability sosai gaban Al'umma Adamawa State...


Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE