An yaba da yadda aka gudanar da zaben shuwagabanin kananan hukumomi a jahar Adamawa.

 





An kammala zaben shuwagabanin kananan hukumomin Mubi ta Arewa da Mubi ta kudu dake jahar Adamawa lafiya ba tare da matsalaba.



Mashawarci na musamman kan harkokin jama a wa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jahar Adamawa Barista Sunday Wugira ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai Jin kadan bayan ya ya duba yadda zaben ya gudana a cikin kananan hukumomin biyu.



Barista Sunday Wugira yace komai ya tafi yadda ya kamata Kuma Al umma sun fito sosai domin su kada kuri arsu  Wanda Kuma kowa yayi zabensa lafiya ba tare da tada nijiyar wiyaba.



Barista Sunday ya Kara da cewa dukkanin mazabu da ya duba ya tarar da malamain zabe na gudanar da aiyukansu cikin tsanani Suma masu kada kuri a na gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali ba tare da hayaniyaba.



Da wannan nema yake yabawa hukumar zabe maizaman kanta ta jahar Adamawa bisa na mijin kokari da tayi na shirya ingancaccen Zabe a fadin jahar.



Wugira ya Kuma jinjinawa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa rawa da ya taka na ganin an gudanar da ingancaccen Zabe da Kuma adalci a fadin jahar, saboda haka Yana da muhimmanci daukacin Al umma jahar Adamawa su baiwa gwamnatinsa hadin Kai da goyon baya domin ganin ya samu nasaran gudanar da aiyukan cigaban jahar baki Daya.



Ya yabawa hukumomin tsaro bisa kokari da sukayi na ganin anbi doka da oda wajen kada kuri a Wanda hakan ya taimaka wajen gudanar da zaben lafiya.


Harwayau Sunday Wugira ya shawarci Al umma jahar Adamawa da sukasance masu hada kansu da yin adu o I a Koda yaushe domin wanzar da zaman lafiya a fadin jahar dama kasa baki Daya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.