Inganta tsaro: Rundunan tsaron Civil Defence a jahar Adamawa ta shiryawa Jami anta bita.

 






A kokarinta na inganta aiyukanta Rundunan tsaron bada kariya ga fararen hula wato Civil Defence shiyar jahar Adamawa, ta shirya bita ta musamman ga Jami anta dake fadin jahar Adamawa





Kakakin rundunan a jahar Adamawa DSC Nyako Amidu Baba ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.




DSC Amidu Nyako yace an dauki matakin hakane saboda inganta aiyukan rundunan a wani mataki na Samar da wadaceccen tsaro domin wanzar da zaman lafiya a fadin jahar baki Daya 





DSC Nyako yace yin haka zaitaimaka wajen dakile kalubalen tsaro da ake fuskanta da Kuma cigaban zaman lafiya.




DSC Amidu ya Kara da cewa duba da yanayi tsaro da ake fama da shi hakan yasa even ndunan ta dauki mataki horar da Jami anta kamar yadda Babban  kwamandan rundunan na kasa Abubakar Ahmed Audi ya bada umurni Wanda a yanzu haka ana gudanar da irin wannan bita a dukkanin fadin Najeriya.




Saboda haka nema rundunan a jahar Adamawa ta gaiyato Jami anta dake ofishoshinta dake kananan hukumomi 21 dake fadin jahar Adamawa.




Ya Kuma baiyana fatansa dangane da wannan horo Wanda acewarsa Yana da muhimmanci Jami an suyi amfani da abinda aka kiya musu domin ganin sun samu cigaban aiyukansu yadda ya kamata.





Da wannan ne yake shawartan Al umma da a Koda yaushe sukasance masu baiwa rundunan hadin Kai da goyon baya domin ganin ta samu nasaran kare rayuka da dukiyoyin Al ummah.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

TETFund Director Commends MAUTH Doctors Over Successful Separation of Conjoined Twins