Kungiyar FOMWAN a jahar Adamawa ta kudiri aniyar rage yaranda basa zuwa Makaranta.
Kungiyar mata musulmai ta tarayya wato FOMWAN shiyar jahar Adamawa ta lashi takwabin ganin an samu raguwar yaran da sa zuwa Makaranta a fadin jahar.
Amira kungiyar ta FOMWAN a jahar Adamawa Hajiya Khadija Buba ce ta baiyana haka a zantawarta da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Hajiya Khadija Buba tace sun dauki matake daban daban domin ganin an shiyar da yara makarantu domin su samu inganceccen illimi a wani mataki na ganin kowane yaro Yana zuwaakaranta.
Hajiya Khadija tace Yana daga cikin matakai da suka dauka na baiwa yara gurbin karatu da Kuma hada Kai da iyaye domin tattaunawa da Kuma nuna musu muhimmanci tura yara Makaranta maimakon baransu a gida.
Saboda haka ne ma take Kara jaddada kiranta ga iyaye da suyi dukkanin maiyiwa domin tabbatar da ganin yaransu sun shiga Makaranta, Wanda hakan zai taimaka wajen kawo karshen matsalar yaran da basa zuwa Makaranta.
Hajiya Khadija tace FOMWAN ta kimtsa tsaf domin ganin tayi dukkanin abinda suka dace domin kawo karshen matsalar baki Daya.
Itama anata bangaren mataimakyar Amiran Amma Goni Mu azu tace kungiyar ta FOMWAN ta na aikine da kungiyoyi masu zaman kansu domin ganin an baiwa yaran illimi Mai nagarta.
Don haka ne ma take kira ga masu ruwa da tsaki da su zo a dama dasu cikin harkokin baiwa yaran illimi ko ahigar da su Makaranta.
Ta Kuma kirayi shuwagabanin da suma su tashi tsaye wajen gudanar da aiyukan da suka dace domin Kai yara makarantu.
Itama shawartan iyaye tayi da sukasance suna tura yaransu makarantun domin ganin an samu saukin lamarin domin a cewarta iyaye sune suke da kaso mafi tsoka wajen kula da Kuma tura yara Makaranta.

Comments
Post a Comment