Mai baiwa gwamnan jahar Adamawa shawara akan harkokin tsaro ya samu lambar yabo.
A kokarinsa na ganin an inganta zaman lafiya da tsaro a jahar Adamawa mashawarci na musamman akan harkokin tsaro ga gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jahar Adamawa Ahmed Lawan ya samu lambar yabo daga wata kungiyar APRM ta Bashi
Da yake jawabi Jin kadan da karban lambar yabon Hon. Ahmed Lawan ya baiyana jindadinsa dangane da wannan lambar yabo da ya samu tare da yin alkawarin cigaba da yin dukkanin abinda suka dace domin ganin an samu zaman lafiya a jahar Adamawa baki Daya.
Ahmed Lawan ya baiyana cewa gwamnatin jahar Adamawa karkashin jagoranci gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ta lashi takwabin ganin an wanzar da zaman lafiya dama inganta tsaro da Kuma gudanar da aiyukan cigaba.
Ahmed Lawan ya Kuma jaddada cewa aniyarsa na ganin Al ummar jahar Adamawa sun zauna lafiya harma da inganta tsaro harma da lafiyarsu yadda ya kamata.
Ahmed Lawan yace gwamnatin jahar Adamawa karkashin jagoranci gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ta kimtsa tsaf domin kare rayuka dama dukiyoyin Jama a.don haka nema Ahmed Lawan yake kira ga daukacin Al ummar jahar Adamawa da sukasance suna baiwa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri hadin Kai da goyon baya domin ganin ya samu nasaran cigaba da aiyukan cigaba da yajeyiwa jahar Adamawa .
Ahmed Lawan ya godewa kungiyar ta APRM bisa wannan lambar yabo da ta Bashi wannan hakan zai karamasa karfin gwaiwar cigaba da aiyukan wanzar da zaman lafiya da yakeyi.

Comments
Post a Comment