Makarantar NA IBI Academy ta yaye dakibenta 27 karo na biyu a jahar Adamawa.









Makaranta NA IBI Academy makarantace dake Karantar da haddar Al Qur ani Mai girma a cikin shekara Daya.



Da yake magana a yayin bikin yaye daluben gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri Wanda sakataren gwamnantin jahar Adamawa Barista Auwal Tukur yace anata bangaren gwamnati tana iya kokarinta domin ganin an samu cigaba wajen bunkasa karatun Al Qur ani maigirma.




Gwamnan ya Kuma yabawa Sheirk Abdullahi Bala Lau bisa kokarinsa na bude wannan Makaranta ta haddar Al Qur ani maigirma.



Don haka nema yake shawartan iyaye da sukasance masu Kai yaransu makarantu koyon asdini da zamani domin samun cigaban ilimin addini yadda yakamata.




Shima a jawabinsa Sheirk Abdullahi Bala Lau baiyana godiyarsa yayi ga iyaye daluben yayi bisa goyon baya da suke baiwa Makaranta don haka ya bukacesu da sucigaba da baiwa Makarantar hadin Kai da goyon baya domin  acewarsa haka zai taimaka wajen cigaban Makarantar 




Sheirk Bala Lau ya Kuma jaddada aniyarsa nayin dukkanin maiyiwa domin bunkasa haddar Al Qur ani maigirma a tsakanin Al umma musulmai.




Sheirk Abdullahi yace saboda haka nema kawo yanzu akwai makarantu yadda Al Qur ani maigirma a sassa daban daban dake fadin Najeriya domin ganin an baiwa matasa da ma yara damar haddar Al Qur ani a duk inda suke.




Ya Kara da cewa Makarantar NA IBI tana baiwa daluben haddar Al Qur ani a cikin shekara Daya dak saboda haka iyaye su Kara kaimi wajen tura yaransu Makarantar domin su samu haddar Al Qur ani maigirma yadda yakamat.





Da yake jawabi Babban bako Sheirk Abdulkadir Saleh Kazaure ya baiyana irin gumawa da makarantu haddar Al Qur ani ke bayarwa da Kuma cigaba da ake samu Wanda acewarsa yanzu hakama an samu daluben da dama wadanda suka had dace Al Qur ani a sassa daban daban dake Najeriya.




Ya yabawa Sheirk Abdullahi Bala Lau bisa na mijijn kokari da yayi na Samar da irin wadanan makarantu da dama don haka akwai bukatar iyaye su bada hadin Kai da goyon baya Wanda a cewarsa iyaye suna da gudumawa da zasu iya bayarwa wajen haddar Al Qur ani maigirma.




An dai bada lambobin yabao wadanda suka hada da sheirk Abdullahi Bala Lau da makamai, da dai sauransu.




Akalla daluben ashurin da bakwau ne dai a aka yaye wadanda sukayi haddar Al Qur ani Mai girma a Makarantar ta NA IBI a wannan shekara ta 2024.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

TETFund Director Commends MAUTH Doctors Over Successful Separation of Conjoined Twins