HUKUMAR CI GABAN YANNKIN AREWA MASO GABAS TA TALLAFAWA WADANDA ISKA TA SHAFA A JAHAR ADAMAWA
By
Babangida Galleon
Hukumar ci gaban yankin arewa maso gabas, NEDC ta raba wasu kayakin tallafi ga marasa galihu da wadanda barnar iska ta shafa a jahar Adamawa.
Yayin rabiyan wanda akayi a birnin yola, fadar jaha mataimakin manaja a sashin jigila da daidaituwa, Malam Lawan Hamidu yace hukumar tayi imani cewa aikin jinkai bai tsaya kawai a samar abubuwa kawai ba, akwai maido da mutunci da kyakkyawar yakini, da dai sauran su..
Mataimakjn manajan, Lawan Hamidu yayi bayanin cewa a ko da yaushe, hukumar ci gaban yankin arewa maso gabas na tabbatar da cewa an hango marasa galihu dake al'umma, an ji su ,an kuma tallafa musu.
"a dan makonni i da suka shige an yi wata iska a jahar Adamawa wanda ta lalata gidaje tate da jefa mutane da dama cikin wata hali"
Lawan Hamidu yace maxauna yankuna da iskar ta shafa musamman marasa galihu, abun ya shafe su sosai shi yasa hukumar ta kawo musu wannan dauki.
Da wannan kuma Ya bukaci da su amshi wannan tallafi a matsayin wata yunkurin taimakawa daga hukumar.
Tun farko dai a jawabin ta na maraba, jami'ar kai komon hukumar na riko a jahar Adamawa, Hajiya Fatima Bakari tayi bayanin cewa hukumar ci gaban yankin arewa maso gabas ta gudanar da muhimman aiyukan ci gaba a bangarorin gine gine, noma da kiwon lafiya a jahar Adamawa.
"a bangaren noma kuwa, mun samar da kayakin noma da zasu taimaka gurin habaka harkar noma domin inganta rayuwan al'umma "
Wakilan kungiyar mabiya addunin krista CAN, da na majalisar musulmai ,Muslim council , da kuma shugaban kungiyar masu bukata ta musamman ta kasa reshen jahar Adamawa, Victor Sajoh da Abdullahi Toungo sun yaba da kokarin hukumar na tallawa a ko wani lokaci nusamman a lokacin da ake fama da wahala.
"a duk lokacin da za ku bada wani tallafi, kuna bamu kuma muna yaba muku da wannan kokari"
Kayakin abinci davaka raba sun hada da katon na taliyar indomi guda dubu uku, Sai katon na supageti dubu biyu da dari daya, da kuma gallon na main girki guda dubu foma sha shidda
Comments
Post a Comment