Kungiyar makuta na musamman ta rantsar da sabbin shuwagabaninta a jahar Adamawa.
An ratsar da sabbin shuwagabanin kungiyar masu bukata na musamman bangaren guragu Wanda da zasu jagoranci kungiyar na tsawon shekaru masu zuwa.
Bikin rantsar da sabbin shuwagabanin dai ya gudana ne a harabar sakatariyar kungiyar dake Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
A mako da ta gabata ne dai kungiyar ta gudanar da zaben sabbin shuwagabanin wadanda suka tsaya ba tare da abokan hamaiyyaba. Wanda ya gudana cikin kwanciyar hankali.
Da yake jawabi Jin kadan da rantsar da su shugaban kungiyar Abdullahi Tongo Wanda ya dawo a WA adi na biyu, ya baiyana godiyarsa da Jin dadinsa dangane da rantsar da su, ya yabawa kwamitin shirya zabe bisa na mijin kokari da sukayi na ganin komai ya tafi dai dai na tare da wata matsalaba.
Abdullahi Tongo yayi alkawarin tafiya da kowa a matsayin tsintsiya madaurinki Daya, don haka nema yake kira ga membobin kungiyar su baahi hadin Kai da gogin baya domin ganin sun samu nasaran gudanar da aiyukan cigaban kungiyar yadda ya kamata.
Ya Kuma yabawa gwamnatin tarayya dangane da yadda ta baiwa mabukata na musamman kaso biyar a gurbin Samar da aiki. Da wannan nema yake kira ga gwamnatin jahar Adamawa da ta baiwa mabukata na musamman kaso biyar na gurbin ma aikata, Wanda a cewarsa hakan zai taimaka musu wajen cigaban kungiyar baki baki Daya.
A jawabinsa na maraba shugaban hadakar kungiyar mabukata na musamman a jahar Adamawa Injuniya Sani Sabo ya Yaba da yadda aka gudanar da zaben da Kuma bikin rantsuwar wanda acewarsa hakan ma cigaba ne yadda ya kamata.
Ya kirayi daukacin membobin kungiyar da sukasance masu hada kansu a Koda yaushe domin samun cigaban kungiyar ba tare da matsalaba.
Bikin ya samu halartan bikin jama a da dama wadanda suka fito daga kungiyoyi daban daban dama wakilain Yan siyasa da dama daga sassa daban daban.
Barista Simon ne dai ya jagoranci rantsar sabbin shuwagabanin tare da kiransu da sukasance masu gudanar da aiyukansu bilhakki da gaskiya da Kuma bin doka yadda ya kamata.
Comments
Post a Comment