Yan Agaji suna taimakawa wajen kiwon lafiya.

 








An baiyana cewa Yan Agaji suna taka mahimmiyar rawa wajen taimakawa Al umma baki Daya.




Darektan yàn Agaji na kungiyar jama Atul izalatul Bid a wa ikkamatun Sunnah Mai shelkwatan a Jos shiyar jahar Adamawa Alhaji Ibrahim Jalo ne ya baiyana haka a zantarwarsa da jaridar An Nur Hausa a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.



Alhaji Ibrahim Jalo yace Yan Agaji suna taimakwawa Al ummah ta bangarori daban daban da suka hada da kiwon lafiya, harkokin ilimi, harma da bangaren addini irin su daidaita sahu da dai sauransu.




Alhaji Jalo yace saboda haka nema suke shiryawa Yan Agaji bitoti daban daban harma da attisaye a shekara shekara tare da gaiyato kwararru a bangarori daban daban, domin sanin makaman aiki yadda ya kamata.




Da wannan ne yake kira ga matasa da su kasance suna shiga Agaji domin su bada tasu gudumawa wajen cigaban Al umma dama addini da dai sauransu.




Ya Kuma shawarcesu da sukasance masu hada kansu da Kuma Neman ilimi na addini Dana zamani domin samun cigaban aiyukansu ba tare da samun matsaloliba.





Ya kiragi Al umma da sukasance suna baiwa Yan Agajin hadin Kai da goyin baya a lokacinda suke gudanar da aiyukansu a ko Ina domin ganin sun cimma burinsu na taimakawa Al ummah a cikin da wajen jahar Adamawa.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT