FOMWAN N TA TAIMAKAWA MARASSA GALIHU DA KAYAKIN ABINCI A JAHAR ADAMAWA..
Daga Alhassan Haladu Yola.
Kungiyar mata musulmai a Najeriya FOMWAN Shiyar jahar Adamawa ta rarranawa marassa galihu kayakin abinci domin Samun saukin rayuwa a cikin wannan watan na Azumin Ramadan.
Amira FOMWAN a jahar Adamawa Hajiya Khadija Buba ce ta baiyana haka a lokacin suke rabon kayakin a harabar makarantar dake Yola.
Hajiya Khadija tace sun rarraba kayakin ne biyo bayan tallafi daauka Samun daga wurare daban daban Wanda Kuma hakan ne ya Basu kwarin gwiwar tallafawa marassa galihu domin Suma su Samu abinci zasuyi amfani dashi a cikin wannan wata na azumi.
Saboda haka nema take Kiara ga kungiyoyi masu hanu da shuni gwamnatoci da sukasance suna taimakawa marassa galihu, marayu, mabukata na musamman da dai sauransu domin Suma su samu saukin rayuwa.
Hajiya Khadija ta Kuma kirayi jamma a da sukasance masu Neman abinda zasu dogara da kansu domin samu cigaban da Kuma Samun saukin rayuwa yadda ya Kamata.
Ta Kuma godewa gwamtain jahar Adamawa karkaahin jagorancin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa taimakawa da yaiwa FOMWAN da kayakin abinci daban daban Wanda a cewarta hakan nema yasa su ka Samu damar rarraba kayakin ga mabukata.
Ta kirayi Wanda suka Samu kayakin da suyi amfani da su yadda ya Kamata na tare da wata kumbiya kumbiyaba, domin ganin sun inganta rayuwarsu.
Wasu daga cikin wadanda suka samu kayakin sun baiyana farin cikinsu tare da godiyarsu dangane da wannan taimako da FOMWAN din ta musu tare da tabbatar da cewa zasuyi amfani da shi yadda ya dace.

Comments
Post a Comment