IMWON ta rabawa marayu kayakin abinci domin Azumin Ramadan a Jahar Adamawa..

 




Daga Alhassan Haladu Yola.


An shawarci iyaye marayu mata da sukasance masu rike marayun bisa gaskiya da rikon Amana domin su kwana da sanin Allah madaukakin sarki zai tambayaesu ranan gobe kiyama.


Amira kungiyar mata musulmai a Najeriya IMWON Shiyar jahar Adamawa Hajiya Asma u Abubakar ce ta Bada wannan shawara a lokacin da suke rabawa marayu kayakin abinci Wanda ya gudana a Yola.


Hajiya Asma u Abubakar tace rikon marayu abune da yake da Lada mai yawa don haka akwai bukatan iyaye mata su Maida hankali sosai kan rikon maraya domin ganin ya tashi cikin tarbiya yadda ya Kamata.



Malama Asma u ta Kuma kirayi iyayen da sun Sanya yaran marantar addini Dana zamani domin ganin sun tashi da illimi addini da na zamani Wanda hakan zai taimaka musu wajen inganta rayuwarsu ba tare da matsalaba.



Ta kirayi marayun da Suma su Maida hankali wajen karatu da Kuma bin iyaye sau da kafa tare da jajircewa wajen yin duk abinda zai taimakawa rayuwarsu ba tare da wata matsalaba.



Hajiya Asma u tayi gargadi ga iyayen marayun mata da kada su sayar da abinda aka basu, suyi amfani da su ta hanyar da ta dace, Kuma sukasance masu wadatar zuci Wanda haka zai tai maka musu wajen rufawa kansu asiri.



Itama anata jawabinta Hajiya Aishatu Ibrahim ta bukaci marayun da sukasance masu Sanya tsoran Allah a zukatarsu da Kuma yiwa iyaye da a Wanda hakan zai taimaka musu wajen inganta rayuwarsu a tsakanin Al umma.


Ta Kuma kirayi kungiyoyi, Yan kasuwa, dai dai Kun jama a da sukasance masu taimakawa marayuwa domin ganin Suma sun Samu saukin rayuwa yadda ya Kamata.


Dukkaninsu dai sunyi Adu ar Allah madaukakin sarki ya hafaratwa iyayen su da suka rasu yasa Kuma Aljannace makomarsa.


Wasu daga cikin iyayen marayun sun baiyana farin cikinsu dangane da wannan taimako da IMWON tayi musu Kuma da yardan Allah zasuyi amfani da shi ta hanyar da ta dace.


Cikin kayakin da aka rarraban dai sun hada da shinkafa kayan sawa da dai sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.

ADAMAWA STATE POLICE COMMAND CELEBRATES WOMEN POLICE @ 70