Majalisar Addinin musulunci a jahar ADAMAWA ta shiryawa mabukata na musamman Buda baki.

 






Daga Alhassan Haladu Yola.


Majalisar Addinin musulunci dake jahar Adamawa ta shiryawa mabukata na musamman Buda baki Wanda ya gudanar a sakatariyar majalisar dake Yola.


Da yake jawabi Jin kadan bayan Buda bakin shugaban majalisar Addinin musulunci a jahar Adamawa Mallam Gambo Jika yace dalilinsu na shiryawa mabukata na musamman Buda bakin ne domin ganin an Samu kyakkawar halaka da Kuma hadin Kai a tsakanin mabukata na musamman da sauran Al umma.


Mallam Gambo Jika ya Kuma tabbatarwa mabukata na musamman cewa majalisar a shirye take su tafi kafada da kafada wajen yin dukkanin abinda zai kawo cigaban a tsakanin mabukata na musamman dama sauran Jama a.


Mallam Gambo ya Kuma kirayi gwamnatin tarayya dana jiha da su aiwatar da dokan da zai samarwa mabukata na musamman dokan da zata samarwa mabukata na musamman Hukumar da zata inganta walwalar su yadda ya Kamata ba tare da wata matsalaba.


Ya Kuma ja hankalin Al umma da sukasance masu mu amala da mabukata na musamman domin Suma Yan Adam ne kamar kowa don haka ya Kamata a jawosu a jiki domin ganin an rage musu yawan tunani.


Ya shawar cesu da su dauki wannan matsala a mazatin kaddara ne daga Allah domin Allah Yana jaraba bayinsa da abubuwa daban daban.


A jawabeau Abdullahi Njidda Damare da Mallam Ahmed Tahir sun bukaci mabukata na musamman da sukasance masu hakuri a Koda yaushe da Kuma hada kansu domin ganin an Samu cigaban kungiyar ta su dama inganta rayuwarsu.


Daga bisanin dai majalisar da baiwa mabukata na musamman kyaututuka yaduna da turamen zani domin Suma su gudanar da bukuwar Sallah kamar kowa.



Wasu daga cikin mabukata na musamman din dai sun baiyana godiyarsu da farin cikinsu dangane da wannan karramawa da majalisar Addinin musulunci jahar Adamawa ta shirya musu Wanda hakan ya Nuna musu cewa ana tare da su yadda ya Kamata.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie