WOMEN IN DA AWA TA TAIAMAKAWA MAZAUNA GIDAJEN YARI DA MARASSALAFI DAKE ASIBITI.

 




Daga Alhassan Haladu Yola.


Kungiyar Women in Da awa dake jahar Adamawa ta taimakawa mazauna gidan yari da marassa lafiya dake Asibitin kayakin abinci da sauramsu a Wani mataki na Samar musu da saukin rayuwa a cikin wannan wata na Azumin Ramadan.


Kungiyar ta Women in Da awa ta ziyarci gidajen yarin dake cikin garin Jimeta dake karamar Hukumar Yola ta arewa da gidan yari dake yolde pate a karamar Hukumar Yola ta kudu wadanda ke jahar Adamawa.


Da take jawa a gidajen yarin Hajiya Aishatu Babasiya Wanda ita cema mai Hulda da jama a a kungiyar ta Women in Da awa a jahar Adamawa. Ta kirayi mazauna gidan yari da sukasance masu canja halayensu Kuma su dauki zamanau a gidan yari a matsayin darasi Wanda Allah yasa sun fita baza su sake komawaba.


Ta Kuma ja hankalinau da sukasance masu yiwa shuwagabanin gidajen yarin biyayya da Nuna da a domin ganin sun Samu rayuwa mai ingancin, tare da ahawartansu da su Kara himma wajen yin ibada musammanma acikin kwanaki goma na karshen watan Ramadan domin Neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen fitar da su daga yanayinda suka tsinci kansu.


A ziyaran da suka Kai a asibiti kuwa Women in Da awa yayiwa marassa lafiya Adu o I na musamman domin Neman Allah Madaukakin sarki ya Basu lafiya domin ganin sun gudanar da rayuwarsu yadda ya Kamata.


Tare da kiransu da Suma su dukufa wajen yin Adu o I domin Samun sauki domin ganin sun koma gidajenau cikin koshin lafiya.


Sun Kuma yabawa jami an asibiti bisa yadda suke baiwa marassa lafiya kula yadda ya Kamata.


Wasu daga cikin marassa lafiya sun yabawa kungiyar ta Women in Da awa dake jahar Adamawa bisa wannan taimako da suka kawo musu, Wanda acewarsu hakan ya taimaka kwarai.


Cikin kayakin da sun hada da shinkafa mai da dai sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.

TETFund Director Commends MAUTH Doctors Over Successful Separation of Conjoined Twins