A yayinda aka fuskanci Babban zaɓen shekara ta 2027 an kirayi matasa da mata da su tabbata sun mallaki katin zabe.

 











Daga Alhassan Haladu Yola.

Domin an dama da su a harkokin Siyasa an kirayi matasa da mata da su tabbata sunje suyi rijistan katin zabe, ga wadanda sukayi rijista kuwa su tabbatar sun karbi katin zabe su Wanda hakan ne zai basu damar zaban shuwagabanin da suke so a lokacin Babban zaɓen shekara ta 2027.


Mrs Comford Ibrahim Wanda itace Ko odinatan mata a siyasa wato women in politics dake Yan kin arewa masau gabasa ita tayi wannan Kira a zantawarta da manema labarai a Yola.



Mrs Comford Ibrahim tace mata da matasa sune suke da Kaso Mafi tsoka a kada kuri a don haka ta jaddada kiranta ga mata da matasa da kada suyi kasa a gwiwa wajen yin rijistan katin zabe domin da katin ne za su zabi Wanda zai cire musu kitse a wuta.



Mrs Comford ta Kuma shawarci mata da matasan da kada wasu su rudesu ranan zabe da abinda ba zai magance musu matsalar suba su tabbata sun zabi shugaban da zai kare musu martanarsu dama sama musu aikinyi.


A cewar Mrs Comford dai mata da matasa sun gaji da gafara sa ba suga kahoba saboda haka gari ya waye musu ba zasu yarda a yaudaresu ba za su tsaya ysayin daka domin tabbatar da ganin sun zabi shugaban mai tausayin takalakawa.



Ta Kuma Kara da cewa baza ta daina Kiran Yan siyasa ba dangane da baiwa mata Kaso mai tsaka a cikin majalisun dokokin kasa Dana jihohi harma da mukamain gwamnati Wanda a cewarta mata na irin mukamain da baza su iya rikewaba.


Saboda haka duk jam iyun da mace ta fito takara to a marabata baya domin itama ta Bada nata gudumawa wajen hadin Kai, zaman lafiya da Kuma cigaban kasa baki Daya.


Mrs Ibrahim ta shawarci mata da matasan da sukasance masu hada kansu wake guda da Kuma yin dukkanin abinda zai kawo zaman lafiya da hadin kan Al umma baki Daya.

Comments

Popular posts from this blog

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.