Dan Takararmu Na Gwamna ba Makaryaci ba ne....Dr Ahmed Gana
By Abdullahi Tukur
Dr. Jamil Isyaku Gwamna, Sardaunan Gombe, ba sabon suna ba ne a fagen siyasar Jihar Gombe. A duk inda kaji an kira sunansa, babu abinda yake biyo baya face, Nagarta, Aminci, Yabo, Jinjina da Sambarka.
Dr Ahmed Gana, tsohon kwamishinan lafiya na Jihar Gombe ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Gombe.
Sardauna ya kasance Dan Jihar Gombe daya fito daga gidan manya wanda hakan ya bashi damar samun kyakkyawar tarbiyya da Ilimi mai nagarta. Jamil Gwamna Mutum ne mai hidima ga al'umma ga kyauta ga kuma son jamaa, kamar yadda mahaifinsa yake.
Sardaunan Gombe Mutum ne mai kishin jiharsa, mai son ci gabanta, kuma wanda ya shafe shekaru sama da 20 yana gina kyakkyawar alaka da al’ummar jihar tare da bayar da gudummawa wajen inganta rayuwar matasa da sauran jama’a.
Sardauna mutum ne mai ilimi da kwarewa. Dokta ne a fannin tattalin arziki, kuma gogaggen ma’aikaci da ya yi aiki a hukumomin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu. Wannan kwarewa ta ba shi fahimtar yadda ake tafiyar da tattalin arziki, samar da damammaki da kuma sarrafa albarkatu domin amfanin jama’a.
Baya ga ilimin zamani, Sardauna mutum ne mai ilimin addini, hakuri da jajircewa, ga tausayi, mutunta mutane da girmama kowa—daga sarakuna da malamai zuwa ’yan kasuwa da matasa. Ya fahimci cewa shugabanci ba mulki ba ne kawai; amanar jama’a ce da ake bukatar a rike ta da gaskiya, adalci, amana da kishin kasa.
A cikin shekaru da dama da ya shafe yana cikin harkokin siyasa a Gombe, Sardauna ba a shede shi da karya ko girman kai ba. Sannan, Mutum ne da baya yaudara. Yana da kishin Jihar Gombe, wanda hakan ne ya sa ya mayar da hankalinsa wajen gina rayuwar matasa, taimaka musu wajen samun ayyukan yi, sana’o’i da hanyoyin dogaro da kai. Ya kuma gina alaka mai karfi da manyan sassa na al’umma, lamarin da ya kara tabbatar da cewa siyasarsa ta ginu ne kan mutane, ba kan hayaniya da surutai na kanzon kurege ba.
A yau, abin da ake gani a fili shi ne yadda jama’a ke tashi tsaye domin nemar wa Sardauna kuri’a. Kungiyoyin sa kai na volunteers 1,448 ne ke gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a da neman goyon baya gare shi, suna amfani da lokacinsu, karfinsu da dukiyarsu ba tare da karbar ko sisin kwabo daga Sardauna ba. Wannan ba kawai alamar nasara ba ce; shaida ce ta Nagarta kan yadda jama’a suka yarda da shugabancinsa.
Al’amarin Sardauna sai dai Allah kawai, domin kuwa al’amarin kare martabar Jihar Gombe ne. Nasarar Sardauna kuma ba nasarar mutum daya ba ce; nasarar Jihar Gombe ce baki daya, domin ya samu shaida ta Nagarta, Kwarewa, Jajircewa, Tausayi, Adalci, Sanin Makamar aiki da kuma Rikon Amana.
Dr. Jamil Isyaku Gwamna ba wai yana neman shugabancin Gombe ne kawai ba; yana neman damar yi wa Gombe da mutanen ta hidima ne
A yanzu haka Jihar Gombe na bukatar shugaba mai ilimi dake aiki da Ilimin, kwarewa, hangen nesa, tawali’u da kyakkyawar alaka da jama’a. Gombe na bukatar jagoran da zai hada kan matasa, sarakuna, malamai, ’yan kasuwa da sauran al’umma domin gina jiha mai karfi da tattalin arziki mai dorewa.
Sardaunan Gombe shine mutum daya tilo daya samu wannan shaida ta wadannan siffofi, a don haka, zaben Sardauna shi ne zaben kishin Gombe, hadin kai da makomar jihar.
Sardauna ya shirya. Gombe ta shirya. Lokaci ya yi na Gombe ta zabi jagorancin da ya cancanta.

Comments
Post a Comment