Naja'atu Muhammad; Dantakaran Gwamna a Jihar Gombe Na PDP Makaryaci Ne








Daga Abdullahi Tukur



Hajiya Naja'atu Muhammed ta sake jaddada aniyarta na cewa Dan takaran gwamna a karkashin tutar jam'iyar PDP a jahar Gombe Farfesa Isa Ali Pantami makaryacine.


Hajiya Naja atu ta baiyana hakane a hirarta da BMC Hausa inda tace Bata zauna da wasu ko Waniba  dangane da ta bada hakuri, Kuma babu wata tawaga da sukazo ko ta tura da sunan zata bada hakuri ko ta janye kalamanta, ita bata san wannanba, saboda haka tananan kan bakanta na cewar Farfesa Pantami da mutanensa suna karya.


Dangane da jita jitan cewa wasu sunje da sunan wakilanta da su baiwa Pantami hakuri akan kalaman Hajiya Naja'atu tace bata tura kowaba Kuma basu gaya mataba, saboda haka suma sun zuba karya, don haka it kam ba ta janye kalaman nataba tananan daram akansu.


Hajiya Naja'atu, ta baiyana Pantami a matsayin munafuki, saboda haka ba gudu ba Ja dabaya akan wannan kalaman.


Hajiya Naja'atu Muhammed ta kara da cewar, kowa yana iya yin nashi karya don haka ita Kam ba wadanda ta tura don suje su bada hakuri, ko Kuma wasu suka sameta don ta bada hakuri.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie