Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta ja hankalin matasa da su kaucewa bangan siyasa a yayinda aka fuskanci Babban zaben shekara ta 2027.




Daga Alhassan Haladu Yola.


 Gwamnatin jahar Adamawa ta kirayi matasa da su kaucewa dukkanin abinda zai kawo tashin hankali kafin, lokaci da ma bayan zaΙ“en shekara ta 2027.


Gwamnan jahar Asamawa Ahmadu Umaru Fintiri ne yayi wannan Kira a lokacin da yake jawabi a wurin bikin ranan matasa ta duniya Wanda rundunan jahar Asamawa ta shirya a Yola.


Gwamnan Wanda mai bashi shawara akan harkokin tsaro Hon. Ahmed Lawan ya wakilta. Yace gwamnatin jahar zata shiga kafar Wanda Daya da duk Wanda aka Samu Yana goyon bayan tashin hankali ko Yana da hanu aciki.



Saboda haka matasa kar su bari Wani yayi amfani da su wajen tashin hankali domin cimma burinsa. Domin a cewarsa gwamnatin ba zata nade hanu tana ganin ana tada fitanaba.


Gwamnan ya Kuma kirayi iyaye da Suma su Bada tasu gudumawar wajen fadakar da matasa dangane da illar tada hanakali domin Samar da zaman lafiya mai daurewa a lokaci dama bayan zabe.


A jawabinsa na Bude Taron kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Hassan Kabir Umar yace an shiraya wannan Taron ne bisa umurnin Babban sifeton Yan sandan Najeriya  Olatunji Rilwan Disu domin yani amfani da ranan matasa wajen wayar masu da Kai da su nisanta kansu da aikata laifuka ko bangan siyasa a lokaci dama bayan zabe.



Kwamishinan Yan sandan ya kirayi matasa da suyi amfani da basiran da suke dashi wajen cigaba kasancewa sune shuwagabanin gobe, Kuma sune kashin bayan cigaban Al umma baki Daya.



Acewarsa matasa suna da rawa da zasu iya takawa wajen wanzar da zaman lafiya da cigaba harma da magance tashin hankali a tsakanin jama a .



Shima a jawabinsa Farfesa Jude A Momoduh daga Jami ar Modibbo Adama dake Yola. Kira yayiwa matsan da su sanifa suna da bartaban da Bai makata wasu ko Wani yayi anfani da su wajen tada hankali domin biyan .bukatarsaba saboda haka suyi karatun ta nitsu wajen tafiyar da harkokinsu domin tsira da martabarsu a tsakanin Al umma.



Ya Kuma shawarci Yan siyasa da suyi dukkanin abinda zai kawo cigaban domokiradiya, cigaban zaman lafiya dama cigaban kasa baki Daya.



A sakonsa Babban sifeton Yan sandan Najeriya Olatunji Rilwan Disu Wanda Mataimakin kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa John Sendere ya karanta ya baiyana cewa rundunan Yan sandan Najeriya ta shirya irin wadannan taruka a fadin Najeriya ne saboda ganin an fuskanci Babban zaben shakara ta2027 .



Babban sifeton yace ya zama wajibi a wayarwa matasa Kai da Kuma Jan hankalin su da su nisanta kansu da bangan siyasa da Kuma kar su bari wasu suyi amfani da su wajen tada husuma musammanma a lokacin Zabe, Kuma duk Wanda aka kama ya karya doka to doka zatayi aiki akansa.



Saboda haka ya shawarci matasa da sukasance masu taka tsantsan sukum kaucewa duk abinda zai kawo tashin hankali. Ya Kamata su Bada tasu gudumawar wajen hadin Kai da wanzar da zaman lafiya.



Shima a nashi jawabi shugaban kungiyar matasa a jahar Asamawa kwamiret Ajine delo yace matasa suna taka muhimmiyar rawa wajen hadin Kai da warware matsaloli don haka a shirye suke su Bada gudumawa domin tabbatar da ganin an gudanar da Babban zaben shekara ta 2027 lafiya ba tare da matsalaba.



Ya ja hankalin shuwagabani da su kasance suna Maida hankali kan matasa ta Basu ilimi kauta dama Samar musu da aikin Yi Wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen karawa matasa kwarin gwiwar Bada ta su gudumawar wajen cigaban Al umma.



Kakakin Yan sandan jahar Asamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ya ja hankalin matasa da cewa sune fa shuwagabanin gobe saboda Bai Kamata ace sun zubar da mutumcinsuba.



Itama anata bangaren shugabar kungiyar matan Yan sandan a jahar Asamawa Hajiya Hauwa Hassan Umar Kabir ta kirayi iyaye mata du sukasance suna Maida hankali akan yaransu a Koda yaushe da Kuma Basu tarbiya na gari, Wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen inganta rayuwar matasa.



Taron dai ya Samu halartan kungiyoyin addinai Dana matasa daban daban harma da sarakunan gargajiya, iyaye daga sassa daban daban a yayinda aka tattauna yadda za a dauki matakin domin ganin ba a Samu tashin tashinaba a lokaci dama bayan zabe.

Comments

Popular posts from this blog

π€πƒπ€πŒπ€π–π€ ππŽπ‹πˆπ‚π„ π‚πŽππ…πˆπ‘πŒ 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR π€π‚π‚πˆπƒπ„ππ“ πˆππ•πŽπ‹π•πˆππ† πŒπˆπ‹πˆπ“π€π‘π˜ π•π„π‡πˆπ‚π‹π„ 𝐀𝐍𝐃 π‚πŽπŒπŒπ„π‘π‚πˆπ€π‹ 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie