Al umma Fulani sun yabawa gwamna Fintiri bisa kokarinsa na Samar da zaman lafiya da hadin Kai a fadjn jajha.
Daga Alhassan Haladu Yola.
A madadin Al umma Fulani kungiyar Tabbitel Filaki Jamde Jam foundation a jahar Adamawa ta yabawa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jahar Adamawa bisa kokarinsa na Samar da hadin Kai dama wanzar da zaman lafiya a fadin jahar ta Adamawa.
Shugaban kungiyar Tabbitel Fulaku Jamde Jam Fondation na jahar Adamawa Hassan Ali soja ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a Yola.
Hassan Ali soja yace gwamna Fintiri ya taka rawan ganin wajen shiga tsakanin. Al umma Fulani da shugaban karamar Hukumar Song biyo bayan Wani ta kaddama da ta shiga tsakaninsu a makwanni da suka gabata. Wanda hakan yasa Al ummar Fulani suka kauracewa kasuwar ta song.
Ali soja yace ko da yake lamarin ya faru mai girma gwamna baya gari amma da dawowarsa sai ya tattara daukacin shuwagabanin Al umma Fulani da shuwagabanin gudanarwar mulkin karamar Hukumar ta song, harma da wakilain fadar mai martaba lamidon Adamawa inda aka tattauna tare da warware dukkanin matsaloli dake faruwa a tsakanin bangarorin biyu.
Acewar Hassan Ali dai gwamna Fintiri yayi abin azo a yaba don haka a madadin Fulani ya yabawa gwamna Fintiri bisa na mikin kokari da yayi na sasanta tsakanin bangarorin biyu bayan sun nunawa Juna yatsa.
Ya Kuma Kara da cewa Samun mutum irin gwamna Fintiri sai anyi da gaske domin gwamna ne mai son zaman lafiya da hadin Kai a jaharsa Kuma baison duk abinda zai kawo tashin hankali a fadin jahar.
Don haka suna jinjina masa Kuma suna bashi goyon baya a dukkanin lamuransa domin ganin ya cimma burinsa na Samar da zaman lafiya da hadin Al ummar jahar ta Adamawa baki Daya. Tare da masa Adu ar Alllah ya bashi lafiya da albarkar rayuwa.
Ali soja ya Kuma yabawa Lamido Adamawa bisa yadda wakilain fadar suka halarci tattaunawa domin warware matsalar duk da cewa baya Nan ya tafi duba lafiyarsa, tare da Yi masa Adu ar Allah ya bashi lafiya ya Kuma dawo lafiya,Allah ya bashi nasaran gudanar da sarautarsa lafiya.
Ali soja ya Kuma tabbatar da cewa a wannan mako kasuwar ta song zata koma ci kamar yadda aka Saba Kuma da fatan komai zai tafi dai dai ba tare da matsalaba. Saboda haka kowa yaje ya ci kasuwarsa cikin tsanaki ba tare da wata matsalaba.
Ya Kuma godewa dukkanin wakilain Fulani da suka halarci Taron dama wadanda suka Bada tasu shawarwari dama Jami an gwamnati da suka Bada nasu shawarwari, domin ganin an Samu fahintar Juna da Maka kawo karshen matsalar baki Daya.
Harwayau ya shawarci dukkanin Al ummar Fulani da sukasance masu hada kansu a Koda yaushe da Kuma bin doka da oda tare da kaucewa daukan doka a hanu domin Samar da cigaba dama wanzar da zaman lafiya.
Saboda haka da yardan Allah a mako mai zuwa kasuwar song za a cigaba da saye da sayarwa na tare da fargaba ba.
In za a iya tunawa dai kasuwar ta song jarkokinta ya tsaya cik sakamokon tashin fahintar Juna da ya faru a tsakanin Fulani da shugaban karamar Hukumar ta song.

Comments
Post a Comment