Pantami Ta Tsaya Cak Yayin Da Dubban Jama’a Sukayi Tururuwar Tarbar Jamil Gwamna




Daga Abdullahi Tukur


Gagarumar tarbar da aka yi wa ɗan takarar gwamnan Gombe na APC, Dr. Jamil Isyaku Gwamna, a unguwar Pantami ta rikide zuwa babban taron siyasa, inda maza da mata, matasa da dattawa suka fito domin ganinsa da kuma tarbarsa.


Ibrahim Sani Shawai  Mai Magana da yawun Dan Takarar Gwamna na APC a Jihar Gombe, Dr Jamil Gwamna ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.



Unguwar Pantami da ke cikin birnin Gombe ta dauki hankalin jama’a a ranar Lahadi, yayin da ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar APC, Dr. Jamil Isyaku Gwamna, ya samu tarba mai armashi daga ɗimbin al’ummar yankin.


Dr. Gwamna ya kai ziyara unguwar ne domin ƙaddamar da sabon ofishin kamfen na APC, wanda Alhaji Abdulhamid Jibrin ya buɗe, da nufin ƙarfafa ayyukan yaɗa manufofin jam’iyyar da tattara magoya baya daga mataki na Kasa wato (grassroots)


Sai dai abin da ya fi ɗaukar hankali a wajen taron shi ne yadda ɗimbin jama’a, ciki har da maza da mata, matasa, dattawa da yara, suka fito domin ganin ɗan takarar, lamarin da ya sauya taron buɗe ofishin zuwa wata babbar dama ta nuna goyon baya da sha’awar siyasar Sardaunan na Gombe.


Al’ummar yankin sun nuna farin cikinsu da zuwan Dr. Gwamna, yayin da waɗanda suka samu damar yin jawabi a wajen taron suka bayyana ra’ayinsu cewa shi ne ɗan takarar da suka yi imanin ya fi cancanta da dacewa da shugabancin jihar Gombe.


A nasa jawabin, Dr. Jamil Gwamna ya yaba da tarba ta musamman da al’ummar Pantami suka yi masa, inda ya nuna godiya bisa karamci, girmamawa da goyon bayan da suka nuna masa.


Ya kuma jaddada muhimmancin ci gaba da hulɗa da al’umma kai tsaye, domin fahimtar buƙatunsu da ƙarfafa haɗin kai wajen samar da shugabanci mai amfani ga jama’a.


Taron ya kasance wani ɓangare na ƙoƙarin APC na faɗaɗa ayyukan kamfen da ƙarfafa hulɗa da al’umma a matakin ƙasa, yayin da ake tunkarar babban zaben shekara ta 2027.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

TETFund Director Commends MAUTH Doctors Over Successful Separation of Conjoined Twins