ENGR. AHMAD SALIHIJO AHMAD YA MIƘA TA'AZIYYAR RASUWAR GWAMNA FINTIRI NA GOGGOYARSA TA ƘAƘA




Daga Ibrahim Abubakar Yola.


Ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabun tarayya na Yola ta Arewa, Yola ta Kudu da Girei, Engr. Ahmad Salihijo Ahmad, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga Gwamnan Jihar Adamawa, Mai Girma Rt. Hon. Ahmadu Umaru Fintiri, bisa rasuwar goggo yarsa ta ƙaƙa, Hajiya Halima Mamman Wafudu.



Alhaji Ibrahim Abubakar Darakta, Yaɗa Labarai da Hulɗa da Manema Labarai Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Engr. Ahmad Salihijo Ahmad ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.


A madadin daukacin kwamitin yaƙin neman zaɓensa da al'ummar mazabun tarayya na Yola ta Arewa, Yola ta Kudu da Girei, Engr. Ahmad Salihijo Ahmad ya miƙa saƙon alhini da ta'aziyyarsa ga Mai Girma Gwamna da daukacin iyalansa bisa wannan babban rashi.



Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki (SWT) da Ya gafarta wa marigayiyar kurakuranta, Ya sanya ta cikin rahamarsa, Ya kuma ba ta madaukakin matsayi a cikin Aljannatul Firdaus.



Haka kuma, yana roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya ba Mai Girma Gwamna, iyalan marigayiyar da dukkan waɗanda wannan rashi ya shafa haƙurin jure wannan babban rashi, da ƙarfin zuciya da dauriya.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

TETFund Director Commends MAUTH Doctors Over Successful Separation of Conjoined Twins