FRSC TA KIRAYI MATUKA ABABEN HAWA DA SUKASANCE MASU TAKA TSANTSAN WAKEN TUKI A WANNAN LOLACI NA EMBA MONTHS A JAJAR ADAMAWA.



Daga Alhassan Haladu Yola.


An shawarci Al umma musammanma matuka ababen Hawa da sukasance masu yin taka tsantsan wajen Maida hankali kan abin tujawarsu  musammanma a wannan lokaci da aka yiwa lakabi da Ember Months, Wanda lokaci ne da ake  yawan tafiye tafiye da bukukuwa harma da zirga zirga suwa kasuwanni  domin kaucewa haddura akan manyan hanyoyi da dai sauransu.



Sector Kwamandan Hukumar kare haddura ta kasa FRSC Shiyar jahar Adamawa Sadiq Abubakar Ibrahim ne ya baiyana haka a zantawarsa da mane labarai a Yola.


Sadiq Abubakar Ibrahim yace wannan lokaci, na Ember Months l, lokacine da ake yawan Samun tafiye tafiye da Kuma bukukuwa saboda haka Yana da muhimmanci matuka ababen Hawa sukasance sun Maida hankali wajen tukinsu a key da yaushe Wanda hakan zai taimaka wajen kaucewa aukiwar hadura dake yin asaran rayuka dama dukiyoyin masu yawa.



Sadiq Abubakar ya baiyana cewa Hukumar su ta tashi tsaye wajen Sanya ido da Kuma lura da yadda harkokin ababen Hawa ke gudanar da aiyukansu a sassa daban daban a fadin jahar Adamawa.


Acewar Kwamandan hakan yasa Hukumar ta baza Jami anta a ko Ina wato lunguna da Sako Sako domin tabbatar da ganin ba asamu haduraba a kafin, lokaci dama bayan watannin na Ember Months.


Don haka nema yake Kira ga daukacin matuka ababen Hawa da su sani wannan lokaci, lokacine da ake Samu yawaitar zirga zirga ga Kuma yadda aka fuskanci gangamin yakin Neman zabe saboda haka sukasance masu taka tsantsan a duk lokacin da suke tuki.


Ibrahim ya jaddada aniyar na Hukumar wajen yin dukkanin abinda suka dace domin kare rayuka dama dukiyoyin Al umma a wannan lokaci na Ember Months domin a cewarsa Hukumar ta kimtsa tsaf domin Sanya ido akan manyan dama kananan hanyoyin.



Ya Kuma kirayi  matuka ababen Hawa da sukasance masu bin ka idodin tuki da Kuma dokokin kan hanya Wanda a cewarsa bin ka idodin da dokokin zasu taimaka wajen raguwar hadura dama asaran rayuka dama jikkata da ake Samu alokaci da hatsari ya faru.



Ya shawarci Al umma da sukasance suna baiwa Hukumar hadin Kai da goyon baya domin ganin Hukumar ta cimma burinta na na Samun saukin haddura dama inganta aiyukan tuki yadda ya Kamata.



Watanin na Ember Months dai sun hada da wata satumba, oktoba, nuwaiba da Kuma dissemba, wannan sune watanin da akayiwa lakabi da Ember Months Wanda Kuma lokacine da ake yawan Samun tafiye tafiye da bukukuwa tarurruka da dai sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

TETFund Director Commends MAUTH Doctors Over Successful Separation of Conjoined Twins