Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin farfado da manyan jarin noma a yankunan da rashin tsaro ya shafa





Daga Ibrahim Abubakar Yola.

Gwamnatin Tarayya ta kara kaimi wajen farfado da manyan jarin noma a yankunan da matsalar rashin tsaro ta addaba, inda ta kaddamar da wani sabon tsarin zuba jari da ya hada da samar da tsaro domin dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari da kuma jawo kudaden kamfanoni masu zaman kansu zuwa manyan ayyukan noma.



Shirin ya hada da kamfanin Ministry of Finance Incorporated (MOFI), Integranium Holdings da Defence Agricultural Assets and Projects Development Company (DAPCO), tare da goyon bayan Defence Holding Company Limited, domin hada tsaro, samar da kudaden jari da gudanar da ayyukan noma.


Ana sa ran wannan mataki zai magance daya daga cikin manyan matsalolin da ke hana zuba jari a fannin noma a Najeriya, musamman a yankunan karkara da matsalar rashin tsaro ta hana masu zuba jari saka makudan kudade a harkokin noma da masana'antun sarrafa amfanin gona.



Daraktan zuba jari na MOFI, Dakta Femi Ogunseinde, wanda ke da alhakin kula da tsarin zuba jarin Integranium, ya ce wannan hadin gwiwa zai bai wa gwamnati da abokan huldarta damar tunkarar masu zuba jari da ingantaccen tsarin tsaro domin kare jarin da za su zuba.



Ya bayyana cewa rashin tabbataccen tsarin tsaro ya dade yana kawo cikas ga kokarin jawo jarin cikin gida da na kasashen waje zuwa manyan ayyukan noma, duk da dimbin damar da Najeriya ke da ita a wannan fanni.



Ogunseinde ya bayar da misalan shirin noman waken soya a Jihar Yobe da kuma noman rake a Jihar Jigawa, wadanda ya ce manyan ayyuka ne da za su bukaci jarin biliyoyin daloli, amma nasarar aiwatar da su na da alaka da magance matsalar tsaro.



Ya ce: "Muna da shirin noman waken soya a Yobe, sannan muna da shirin noman rake a Jigawa. Dukkaninsu manyan ayyuka ne da za su bukaci jarin biliyoyin daloli."



A cewarsa, yana da wahala masu zuba jari su amince su kashe makudan kudade a ayyukan noma ba tare da tabbacin cewa za a kare jarinsu, ma'aikatansu da ayyukansu ba.



Ya kara da cewa: "Idan babu ingantaccen tsarin tsaro da zai tabbatar da cewa duk wanda ya kawo jari, za a kare jarinsa, zai yi matukar wahala mu cimma wani abu."



Ya ce hadin gwiwar zai samar da wata kafa ta tattaunawa da masu zuba jari tare da nuna musu cewa an yi la'akari da matsalolin tsaro wajen tsara da aiwatar da ayyukan noman.



Ana sa ran tsarin zai taimaka wajen jawo makudan kudaden jari daga kamfanoni masu zaman kansu da masu zuba jari na kasashen waje, ta yadda za a rage dogaro da kudaden gwamnati, tare da bude hanyoyin bunkasa noman kasuwanci da masana'antun sarrafa amfanin gona.



Yarjejeniyar za ta kunshi kula da hadurra, tsara tsaro da aiwatar da ayyuka, inda DAPCO za ta yi aiki tare da MOFI da abokan huldarta wajen gano, tsara da aiwatar da ayyukan noma masu inganci.



Shugaban DAPCO, Aliyu Abdulhameed, ya ce bangaren tsaro zai taimaka wajen tabbatar da cewa kudaden zuba jari sun isa ga damarmakin noma da ke yankunan karkara cikin tsari mai inganci da tabbacin tsaro.



Ya lura cewa da dama daga cikin ayyukan noma masu riba suna yankunan da ke nesa da manyan birane, lamarin da ya sa tsaro ya zama muhimmin abin dubawa ga masu zuba jari.



Abdulhameed ya ce hadin gwiwar za ta hada karfin kowace hukuma domin bunkasa ayyukan noma da za su kara yawan amfanin gona da kuma habaka tattalin arziki a fadin kasar.



Ogunseinde ya bayyana cewa tuni abokan huldar suka gano wasu damarmakin zuba jari, yana mai cewa yana fatan akalla daya daga cikin ayyukan zai fara gini kafin karshen shekarar nan.



Sai dai bai bayyana sunan aikin da aka zaba domin fara aiwatarwa ba, kuma bai bayar da takamaiman ranar fara ginin ba.



Ya bayyana cewa za a tantance kowanne aiki daban-daban ta fuskar ingancin tattalin arzikinsa, damar samun riba, binciken sahihancin bayanai da kuma tabbatar da cewa kudaden da aka kashe sun dace da amfanin da za a samu.



Baya ga magance matsalar tsaro, an tsara shirin ne domin jawo jari zuwa albarkatun noma na Najeriya, kara yawan abincin da ake nomawa a cikin gida da kuma samar da isassun albarkatun da masana'antu za su sarrafa ko kuma a fitar da su zuwa kasashen waje.



Manajan Daraktan Defence Holding Company Limited, Air Vice Marshal A.V. Ndache, ya ce yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da hukumomin suka sanya wa hannu ta kafa babban tsarin hadin gwiwa wanda ya shafi noma, harkokin otal-otal da sauran damarmakin zuba jari.



Ya bayyana cewa za a rika tattaunawa tare da kulla karin yarjejeniyoyi na musamman ga kowanne aikin yayin da hadin gwiwar ke ci gaba.



Ndache ya ce manufar hadin gwiwar ita ce kara bunkasa ayyukan tattalin arzikin kasa da kuma tallafa wa shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na tabbatar da wadatar abinci a Najeriya.



Haka kuma, Manajan Daraktan MOFI, Dakta Armstrong Takang, ya ce bunkasa noman cikin gida zai taimaka wajen rage hauhawar farashin abinci ta hanyar kara yawan abincin da ake samarwa domin amfanin gidaje da masana'antu.



Ya jaddada bukatar Najeriya ta yi amfani da filayenta, albarkatun ruwa da karfin ma'aikatanta wajen samar da isasshen abinci don biyan bukatun al'ummar kasar, tare da samun rarar amfanin gona da za a iya fitarwa zuwa kasashen waje.



Takang ya ce hadin gwiwar za ta mayar da hankali wajen gano ayyukan noma masu inganci da za su iya jawo kudaden zuba jari daga gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

TETFund Director Commends MAUTH Doctors Over Successful Separation of Conjoined Twins