KUNGIYAR MANOMA ALBASA A NAJERIYA TA TAYA SABON SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR FUFORE MURNAN KAMA AIKI.




Daga Alhassan Haladu Yola.


Kungiyar manoma Albasa da sarrafawa da kasuwacin a Najeriya ta Taya Sabon  shugaban karamar Hukumar Fufore Hon. Yunusa Hammajoda  murna Wanda aka rantsar.


A sakon Taya murna Wanda shugaban kungiyar ta kasa Alhaji Aliyu Isa Maitasamu tare da sakataren Kungiyar ta kasa Alhaji Ibrahim Goni Dasin suka fitar, inda suka baiyana rantsar Sabon shugaban anyishi ne bisa cancanta. Don haka suna tayashi murnan kama aiki a matsayin shugaban karamar Hukumar Fufore.



Sanarwar ta Kuma tabbatar wa Sabon shugaban cewa kungiyar manoma Albasa a shirye take tayi aiki kafada da kafada da Sabon shugaban domin ganin an Samu cigaban bunkasa noman Albasa dama tattalin Arziki a fadin karamar Hukumar dama jaja baki Daya.


Sanarwar ta Kara da cewa a madadin shugaban in kungiyar da membibin kungiyar suna Taya Sabon shugaban murna tare dayi masa fatan Alheri da Kuma Adu ar Allah ya bashi nasaran kammala wa adin mulkinsa lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

π€πƒπ€πŒπ€π–π€ ππŽπ‹πˆπ‚π„ π‚πŽππ…πˆπ‘πŒ 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR π€π‚π‚πˆπƒπ„ππ“ πˆππ•πŽπ‹π•πˆππ† πŒπˆπ‹πˆπ“π€π‘π˜ π•π„π‡πˆπ‚π‹π„ 𝐀𝐍𝐃 π‚πŽπŒπŒπ„π‘π‚πˆπ€π‹ 𝐁𝐔𝐒

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

TETFund Director Commends MAUTH Doctors Over Successful Separation of Conjoined Twins