Rundunan yan sanda a jahar Adamawa tayi nasaran tarwatsa maboyar masu aikata laifuka a jahar.
A kokarinta na dakile aikata ta addanci a fadin jaha rundunan yan sanda jahar Adamawa ta rundunanta dake yaki da aikata laifuka a wasu bangaren jihohin Taraba, Adamawa, Gombe, Yobe, da kuma jahuriyar Kamaru tayi nasaran dakile aiyukan bata gari tare da hadin gwiwar mafarauta. Kakakin rundunan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne dai ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar aka rabawa manema labarai a Yola. Haka kuma rundunan ta samu nasaran kawar da aiyuka masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, fashi da makami, barayin shanu dama dukkanin haramcecen aiyuka akan iyakokin ta Najeriya. Wadanda ake zargin masuyin garkuwa da mutanene da suka ga alamar Jami an tsaro wanda hakan yasa suka ranta ana kare inda aka bude musu wuta wanda hakan yasa wasu suka gudu da raunikan harbi a jikinsu. Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ...