Inganta tsaro: Rundunan tsaron Civil Defence a jahar Adamawa ta shiryawa Jami anta bita.
A kokarinta na inganta aiyukanta Rundunan tsaron bada kariya ga fararen hula wato Civil Defence shiyar jahar Adamawa, ta shirya bita ta musamman ga Jami anta dake fadin jahar Adamawa Kakakin rundunan a jahar Adamawa DSC Nyako Amidu Baba ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. DSC Amidu Nyako yace an dauki matakin hakane saboda inganta aiyukan rundunan a wani mataki na Samar da wadaceccen tsaro domin wanzar da zaman lafiya a fadin jahar baki Daya DSC Nyako yace yin haka zaitaimaka wajen dakile kalubalen tsaro da ake fuskanta da Kuma cigaban zaman lafiya. DSC Amidu ya Kara da cewa duba da yanayi tsaro da ake fama da shi hakan yasa even ndunan ta dauki mataki horar da Jami anta kamar yadda Babban kwamandan rundunan na kasa Abubakar Ahmed Audi ya bada umurni Wanda a yanzu haka ana gudanar da irin wannan bita a dukkanin fadin Najeriya. Saboda haka nema rundunan a jahar Adamawa ta gaiyato Jami anta dake ofishoshinta dake kanan...